19/09/2022
Malamai da Fastoci Sun Gudanar da Addu'a a Cikin Ruwa Kan samun Yardan Allah ha PDP a Zaben 2023
Jam'iyyar PDP reshen jihar Ogun ta koma ga Allah a yayin da ake shirin fara kamfen da gabatowar zaben 2023 An gano malaman Musulunci da fastoci suna rokon Allah alfarma yayin da ruwan sama ke bugunsu Musamman aka shirya taron don neman nasarar jam'iyyar a babban zabe mai zuwa tare da addu'an neman rabuwan kan jam'iyya mai mulki.
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ogun ta mika lamuranta ga Allah inda ta tashi tsaye da addu’o’i kan babban zaben 20023. A wasu hotuna da s**a yadu a intanet, an gano wasu malaman addini durkushe a cikin ruwan sama kamar da bakin kwarya suna masu addu’o’i a garin Abeokuta, babban birnin jihar.
Taron addu’an ya gudana ne a sakatariyar PDP, wanda ke kusa da ofishin Gwamna Dapo Abiodun, jaridar Premium Times ta rahoto.
A wajen taron, mambobin jam’iyya da malaman addinin da s**a yi biris da ruwan sama sun yi addu’a cikin kankan da kai don neman goyon bayan Ubangiji yayin da kamfen da zabe ke kara gabatowa.
Jama’ar wadanda s**a gudanar da addu’o’insu musamman don nasarar jam’iyyar a zaben, sun kuma yi addu’o’in neman raba kan jam’iyya mai mulki, musamman a jihar.
Da yake magana a taron, sakataren jam’iyyar, Sunday Solarin ya ce:
“Koda dai mutane basa yin jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ya zama dole jam’iyyar ta nemi kariya daga masu bita da kulli da za su so tarwatsa shirin da PDP ta rigada tayi.”
Ya kara da cewa shugabannin matan jam’iyyar ne s**a bayar da shawarar yin taron addu’o’in, yana mai cewa ya kasance irinsa na farko da jam’iyyar tayi a jihar Ogun.