AU Online TV

AU Online TV AU Online TV – Real Talk, Real Stories, Real Change. Broadcasting grassroots voices across Adamawa.

DA DUMI DUMI: Wani ɗan Kasuwa ya tafka Mummunar Asara inda ya ajiye Buhun Masara Samada Buhu 3,000 domin tayi tsada  yaf...
05/08/2025

DA DUMI DUMI: Wani ɗan Kasuwa ya tafka Mummunar Asara inda ya ajiye Buhun Masara Samada Buhu 3,000 domin tayi tsada yafito da ita ya Siyar Sai gashi Anje ɗauka Masarar Ta ruɓe gaba ɗaya

Bincike ya tabbatar mana da Cewa Wannan masarar Data lalace Sun boye masarar ne Sabida Suna So Watan Azumin Ramadan yakama kayan masarufi yayi tsada Sai Su fito dashi Su Siyar domin Su ci Muguwar riba sai gashi anzo dauka aka samu ta lalace.

Me Zaku ce?

Waye zai iya fadamuna nan ina ne a cikin garin MUBI, Adamawa State.📸  Niniyo Abubakar
05/08/2025

Waye zai iya fadamuna nan ina ne a cikin garin MUBI, Adamawa State.

📸 Niniyo Abubakar

SHUGABAN GAMBIYA YA KAI ZIYARAR TA’AZIYYA A KAN RASUWAR BUHARIShugaban ƙasar Gambiya, Malam Adama Barrow, ya kai ziyarar...
26/07/2025

SHUGABAN GAMBIYA YA KAI ZIYARAR TA’AZIYYA A KAN RASUWAR BUHARI

Shugaban ƙasar Gambiya, Malam Adama Barrow, ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, inda ya mika sakon jajensa bisa rasuwar tsohon shugaban ƙasar.

Malam Barrow ya roƙi Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya jikansa da rahama, tare da bai wa iyalansa da al’ummar Najeriya hakurin jure wannan babban rashi.

ADC TA GUDANAR DA TARO A ABUJAJam’iyyar haɗaka ta African Democratic Congress, ADC, ta gudanar da wani babban taro a yau...
26/07/2025

ADC TA GUDANAR DA TARO A ABUJA

Jam’iyyar haɗaka ta African Democratic Congress, ADC, ta gudanar da wani babban taro a yau Asabar a birnin tarayya Abuja.

Taron ya tattaro manyan jiga-jigan jam’iyyar daga sassa daban-daban na ƙasa, domin nazari da tsara sabbin dabarun siyasa gabanin zaɓen 2027.

Rahotanni na nuna cewa taron ya kuma mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin kai a cikin jam’iyyar da kuma jan hankalin matasa zuwa harkokin siyasa.

GWAMNA FINTIRI YA SAMU DIGIRIN GIRMAMAWA DAGA JAMI’AR FATAKOLJami’ar Fatakol da ke jihar Rivers ta karrama gwamnan Adama...
26/07/2025

GWAMNA FINTIRI YA SAMU DIGIRIN GIRMAMAWA DAGA JAMI’AR FATAKOL

Jami’ar Fatakol da ke jihar Rivers ta karrama gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, da digirin girmamawa a fannin kimiyyar aikin gwamnati.

Rijistirar Jami’ar, Dakta Gloria Chindah, ta bayyana cewa za a miƙa lambar yabo ne yayin bikin yaye ɗalibai karo na 35 a ranar 26 ga Yuli, 2025.

A jawabinsa, Gwamna Fintiri ya bayyana godiyarsa, yana mai cewa wannan girmamawa za ta ƙarfafa shi wajen ci gaba da aiki tukuru don gina Adamawa da Najeriya.

DALIBAI SUN NUNA AL’ADUN GARGAJIYAR SU A MUBIDaliban Jami’ar Jihar Adamawa da ke Mubi sun gudanar da biki na musamman do...
26/07/2025

DALIBAI SUN NUNA AL’ADUN GARGAJIYAR SU A MUBI

Daliban Jami’ar Jihar Adamawa da ke Mubi sun gudanar da biki na musamman domin baje kolin al’adunsu ta hanyar tufafin gargajiya, kade-kade, da wasannin kwaikwayo.

Bikin ya kasance wata dama ta ƙarfafa fahimta da haɗin kai tsakanin ɗaliban da s**a fito daga sassa daban-daban na Najeriya.

Shugabannin makarantar sun bayyana cewa irin wannan taro na gina zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin matasa daliban

Daliban sun yaba da wannan dama tare da fatan ci gaba da gudanar da bukin a duk shekara.

📸MASS COMM DEPT. ADSU MUBI.

Yarima Al-Waleed bin Khaled bin Talal Al Saud na Saudiyya ya rasu yana da shekara 35.Yayi shekara 20 yana cikin doguwar ...
19/07/2025

Yarima Al-Waleed bin Khaled bin Talal Al Saud na Saudiyya ya rasu yana da shekara 35.

Yayi shekara 20 yana cikin doguwar suma bayan samun mummunan rauni a kwakwalwa sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi a 2005.

Kawo yanzu dai gwamnan yana kan shekarunsa na 6 kane-kane rike da madafun ikon jihar
19/07/2025

Kawo yanzu dai gwamnan yana kan shekarunsa na 6 kane-kane rike da madafun ikon jihar

Ana kara hura wutar neman kafa Jihar Amana, wadda ake son a fitar daga arewacin Adamawa da yankin Uba na jihar Borno.
19/07/2025

Ana kara hura wutar neman kafa Jihar Amana, wadda ake son a fitar daga arewacin Adamawa da yankin Uba na jihar Borno.

Shin Kun ci karo da wannan a shafukan sada zumunta a yau? Meye ra'ayin ku akai?
17/07/2025

Shin Kun ci karo da wannan a shafukan sada zumunta a yau? Meye ra'ayin ku akai?

Address

Alhamdu Bello Way
Mubi

Telephone

+2348058587008

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AU Online TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to AU Online TV:

Share