27/10/2023
WATARANA ALLAH YA TAMBAYI MALA'IKAN MUTUWA😭
Shin baka taɓa yin kuka ba a yayin da kake karɓar ran Ɗan Adam?
Sai mala'ikan yace:
Nayi kuka sau ɗaya, nayi dariya sau ɗaya sannan na firgita sau ɗaya 😢
Sai Allah Yace masa:
Me ya baka dariya ne?
Sai yace: abunda ya bani dariya shine, naje karɓar ran wani mutum sai na iske shi yana cewa mai yi masa takalmi: ka kyautata ƙirar takalman nan, ka ƙira su yadda zan saka su har tsawon shekaru biyar 😢
Sai nayi dariya na ɗauki ransa tun bai saka su ba koh sau ɗaya 😭
Sai Allah Yace masa: toh me yasa ka kuka ya kai mala'ikan mutuwa?
Sai yace:
Abunda ya sakani kuka shine: watarana naje karɓar rayuwar wata baiwar Allah wacce take ita kaɗai a cikin wani babban jeji, da naje sai na iske ta tana haihuwa sai na jira har ta haihu sannan na ɗebe ran nata 😭
Sai kukan jaririn da na bari a jejin shi kaɗai baya da wanda zai kula shi ya sakani kuka 😭😭😭
Sai Allah Yace masa: toh me ya firgitar da kai?
Sai yace: abunda ya firgitar dani shine:
Watarana naje karɓar rayuwar wani malami daga cikin bayin ka sai na iske haske yana fita daga ƙofar ɗakinsa.
Duk lokacin da na kara kusantar ɗakin sa sai hasken nasa ya haska ya mayar dani, sai abun ya firgita Ni 😭
Sai Allah Yace masa: Ya kai mala'ikan mutuwa shin kasan waye wannan mutumen da hasken sa ya firgitar dakai, kasan waye Shi???
Sai yace: A'a!
Sai Allah Yace masa: Wannan mutumen da hasken sa ya firgitar dakai shine Ɗan yaron matar nan da ka ɗauke ranta a jeji ka bar shi shi kaɗai bbu mai kula dashi ✍️
Na kula dashi, na bashi kariya har ya zamo abunda ya firgita ✍️
LA ILAHA ILLALLAH 😭😭😭
TABBAS SHA'ANIN UBANGIJI DABAN YAKE 😭
YA UBANGIJI KAYI MANA SAUQIN FITAR RAI 😭😭🙏
YA ALLAH KA KULA DAMU KUMA KA SHIGA LAMURAN MU KAMAR YADDA KA SHIGA LAMURAN WANNAN JINJIRIN 🙏😭😭 BARKA DA JUMAAT
DAGA NAKU Abdulrashid Monaco