15/04/2026
Honarabul Mahmood Marafa daga Mubi ta Kudu a Jihar Adamawa, ya yi jan hankali kan muhimmancin ƙyale jama’a su zaɓe wanda su ke so, a zaɓen Fidda Gwani na Jam'iyyar APC a Jihar Adamawa, ba tare da samun katsa-landan daga masu ruwa da tsaki ba.