Mubi Times

Mubi Times NAS FM Mubi 105.5

People's Voice
(1)

TSARO: Rundunar Yan sandan Jihar Kwara ta tabbatar da k**a mutane 42 da ake zargi da hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, ...
22/04/2026

TSARO: Rundunar Yan sandan Jihar Kwara ta tabbatar da k**a mutane 42 da ake zargi da hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, biyo bayan sace wani basarake a karamar hukumar Ifelodun ta jihar.

​Kwamishinan Yan sandan jihar, Ojo Adekimi, ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a ranar Litinin, inda yace anyi kamen ne a matsayin wani bangare na kokarin bincikar lamarin da kuma kamo wadanda keda hannu a ciki.

​An sace basaraken ne dai a daren ranar Asabar a gidansa dake garin Olayinka. Adekimi yace jami’an yan sanda, bisa bayanan sirri, sun kaddamar da wani samame na hadin gwiwa wanda ya kai ga k**a wadanda ake zargin.

SIYASAR KANO: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya mika sunan Sule Garo a matsayin Mataimakin Gwamna.Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabi...
22/04/2026

SIYASAR KANO: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya mika sunan Sule Garo a matsayin Mataimakin Gwamna.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mika sunan Murtala Sule Garo a matsayin sabon Mataimakin Gwamna, bayan da Abdulsalam Gwarzo yayi murabus. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar.

Rahotanni sun nuna cewa Gwarzo ya yi murabus ne bayan sabani da gwamnan, wanda ya samo asali daga sauya shekarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC. Hakan ya biyo bayan fara shirin tsige shi da Majalisar Dokokin Jihar Kano tayi.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa nadin Garo yayi daidai da kundin tsarin mulki, kuma an mika sunansa ga majalisar domin tantancewa da amincewa. Garo, mai shekaru 48, gogaggen dan siyasa ne wanda ya taba rike muk**ai daban-daban, kuma ana sa ran nadin nasa zai kara karfafa shugabanci da inganta ayyukan gwamnati a jihar.

Amma shin menene ra'ayin ku. Mu hadu a comment section.

Mubi Times

Ƙoƙarin da ake wajen ganin an warware rikicin dake tsakanin Amurka da Iran tare da kawo ƙarshen yaƙin ya cin tura, bayan...
22/04/2026

Ƙoƙarin da ake wajen ganin an warware rikicin dake tsakanin Amurka da Iran tare da kawo ƙarshen yaƙin ya cin tura, bayan da Tehran ta saya kan batunta na ƙin shiga tattaunawar, a gefe guda Donald Trump ya kafe kan cewa dole sai an cimma matsaya a tattaunawar ne Amurka za ta kawo ƙarshen datse jiragen ruwan Iran a teku.

Wannan na zuwa ne a lokacin da sa'o'i kaɗan s**a rage wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin biyu ya kawo ƙarshe, lamarin da ya sanya fargabar yiwuwar dawowar hare-hare.

Hukumar Hasashen Yanayi a Najeriya tayi gargaɗin yiwuwar ɓullar cutar ɗansankarau  a wasu jihohin Arewacin ƙasar, tare d...
18/04/2026

Hukumar Hasashen Yanayi a Najeriya tayi gargaɗin yiwuwar ɓullar cutar ɗansankarau a wasu jihohin Arewacin ƙasar, tare da yin kira ga hukumomin da alhakin kare lafiyar jama’a ya rataya a wuyansu domin su ɗauki matakan da s**a dace don tunkarar wannan babbar barazana.

Hukumar NiMet ta bayyana jihohin Adamawa, Sokoto, Kebbi da Zamfara a matsayin wasu daga cikin jihohi waɗanda zasu iya fuskantar matsalar ambaliya.

TSARO: Yan bindiga sun farmaki ƙauyen M***a dake Ƙaramar Hukumar Askira Uba dake Jihar Borno,  inda s**a kashe wata mata...
17/04/2026

TSARO: Yan bindiga sun farmaki ƙauyen M***a dake Ƙaramar Hukumar Askira Uba dake Jihar Borno, inda s**a kashe wata mata da sojoji 4 a yayin harin.

Shugaban Ƙaramar Hukumar, Mada Saidu yayin da yake hira da manema labarai, ya bayyana cewa ƴan ta'addan sun kai harin ne da misalin Ƙarfe 12 na ranar Laraba, lamarin da jefa al'ummar ƙauyen cikin fargaba da rashin tabbas na tsaro.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bayanin cewa baya jin tsoron zaben 2027 saboda yadda 'yan adawa s**a yunkuro da karfi a ...
17/04/2026

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bayanin cewa baya jin tsoron zaben 2027 saboda yadda 'yan adawa s**a yunkuro da karfi a jam'iyyar ADC.

Shugaban Yayi martanin ne yayin da yake tattaunawa da jakadun dake yada manufofin shi a fadar shugaban kasa dake Abuja a ranar Alhamis, 16 ga watan Afrilun 2026 Tinubu yayi magana kan girmama umarnin kotu, musamman lura da cewa jam'iyyar ADC ta gudanar da babban taron ta na kasa duk da tana cikin shari'a.

Shugaban Najeriya ya fito da kan shi yana kore jingina masa tsoro da wasu ke yi game da zaben 2027. Hakan na zuwa ne yayin da zabe ke kara karatowa kuma 'yan adawa ke nanata cewa za su fatattake shi daga fadar shugaban kasa a 2027.

Mubi Times

Labarai: Kotu ta bada umarnin k**a tsohuwar ministar jinƙai Dr. Sadiya Umar Farouk saboda zargin bacewar kudi sama da Da...
16/04/2026

Labarai: Kotu ta bada umarnin k**a tsohuwar ministar jinƙai Dr. Sadiya Umar Farouk saboda zargin bacewar kudi sama da Dalar Amurka Miliyan daya da kuma sama da Naira miliyan 746.

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohuwar ministar a gaban kotu tare da wasu jami'anta bayan binciken data gabatar dangane da ɓacewar maƙudan kuɗaɗen.

Cikin waɗanda ake tuhuma har da babban sakataren ma'aikatar a lokacin da Sadiya ke riƙe da muƙamin ministan.

Zarge-zargen da ake yiwa waɗannan mutane ya haɗa da cin amanar ƙasa da zamba cikin aminci hada da bada kwangila ta hanyar da bai k**ata ba da kuma mallake kuɗaɗen hukumar.

Fafaroma Leo ya caccaki shugabanin duniya wajen kashe biliyoyin daloli domin haifar da yaƙi.Shugaban mabiya ɗarikar kato...
16/04/2026

Fafaroma Leo ya caccaki shugabanin duniya wajen kashe biliyoyin daloli domin haifar da yaƙi.

Shugaban mabiya ɗarikar katolikan na duniya ya soki shugabannin dake amfani da addini domin halarta yaƙi, inda ya buƙaci samun sauyi saboda irin ta'adin da ake gani wajen asarar rayuka da kuma dukiyoyin jama'a.

Fafaroma Leo yace waɗannan shugabanni na yaudarar jama'a wajen nuna cewar k**ar basu san irin illar da yaƙin yake haifar wa ba a lokacin da suke kashe biliyoyin daloli, yayin da basa samar da irin waɗannan kuɗaɗe don sake gina al'umma.

Wasu na kalllon wannan jawabi na Fafaroma a kasar Kamaru a matsayin s**a ga shugaban Amurka Donald Trump.

Mubi Times

LABARI CIKIN HOTO:‘Yayan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) sum fara hallara wurin babban taron jam'iyyar na ƙa...
14/04/2026

LABARI CIKIN HOTO:

‘Yayan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) sum fara hallara wurin babban taron jam'iyyar na ƙasa dake gudana a Rainbow Event Centre, Abuja, a ranar Talata.

Hoto: X | African Democratic Congress HQ

KUNGIYAR SERAP TA NEMI MAJALISAR KASA TA BINCIKI SHUGABAN INECKungiyar SERAP ta bukaci Majalisar Dokoki ta Kasa data kad...
14/04/2026

KUNGIYAR SERAP TA NEMI MAJALISAR KASA TA BINCIKI SHUGABAN INEC

Kungiyar SERAP ta bukaci Majalisar Dokoki ta Kasa data kaddamar da bincike mai zurfi kan zarge-zargen da akeyi wa Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC).

Kungiyar ta bayyana cewa lamarin na iya shafar amincewar da jama’a ke dashi ga tsarin zaben dimokuradiyya a kasar.

Kungiyar ta kuma jaddada cewa babu wani jami’in gwamnati da yafi karfin bincike, tare da kira da'a gudanar da binciken cikin gaskiya tare da bayyana sak**akonsa ga jama’a.

Address

Mubi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mubi Times posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share