22/06/2022
GA WASU JERIN MUTANE WADANDA NAKE DA TABBACIN BA ZASU ZABI JAMIYYAR APC KO PDP BA A SHEKARAR 2023
1__ Kasancewar Kwankwaso mai nuna sha'awa kai tsaye wajen inganta harkar ilimi musamman samar da kayan koyo da koyarwa a makarantu da kuma samar da walwala ga malamai musamman a zamanin mulkin sa, sannan uwa uba yadda ya dauki dalibai ya turasu jami'o'i daban daban na gida Najeriya da kasashen ketare. Babu yadda za'ayi rukunin daliban kasar nan musamman na Jami'a su zabi PDP ko APC suna ganin Kwankwaso a jamiyyar NNPP saboda waccan nagarta dana zayyana a sama.
2__ Malaman Jami'a da sauran manyan makarantu; Ganin yadda kullum Gwamnatin APC ke muzgunawa kungiyar ASUU da sauran kungiyoyin manyan makarantu, babu yadda za'ayi wadannan rukunan mutane su zabi APC ko PDP musammam suna kallon Kwankwaso a matsayin wanda ke maida hankali wajen bayar da ingantaccen ilimi. Suna da tabbacin idan ya zama shugaban kasa, zai magance kusan baki daya matsalolin da kungiyoyin ke tafiya yajin aiki domin su.
3__ Zunzurutun matasa masu neman aiki; Wadannan rukunin matasa wadanda sun hada maza da mata kuma sune s**a fi kowa yawa, babu yadda za'ayi ko kusa ko nesa su zabi APC ko PDP saboda yadda s**a kasa magance matsalar samar da aikin yi garesu cikin shekarun da s**a dauka wajen gudanar da mulki a kasar nan.
Ku karo mana wasu rukunan mutanen da dalilan su na kin zabar APC ko PDP a babban zabe mai zuwa na 2023.
Allah ya bawa Kwankwaso shugabancin kasar nan