27/07/2026
DIOMANDE: Daga Mafarkin Rubuta Sunan Ronaldo Zuwa Buga ƙwallon Ƙafa A Ƙungiyar Da Ronaldo Ya Taka Leda
Daga Abubakar Shehu Dokoki
..zuwa ga Æ´an gwagwarmaya da kuma maso É—auke da babban mafarki
Jama'a wannan shine Diomande matashin ɗan ƙwallo ƙafa daga ƙasar Ivory Coast, wanda ƙungiyar Real Madrid ta saya a yanzu.
Ko ba'a faÉ—a maka ba, hotunan sa na Æ™uruciya, sun nuna irin mafarkin daya taso dashi, dakuma irin halin da yake ciki, ma'ana dai "yaro ne talaka kuma mai É—auke da son Ronaldo ko kuma zama k**ar Ronaldo" a ilmin psychology da yawa wanda suke rubuta sunan wani abu a jikinsu, kodai suna da burin zama k**ar sa, kokuma abin yana burge su, shi ya sa wata rana haka kawai sai kaga wani yaron ya zana mota, wani kuma ya zana jirgi, wani kuma sai ya zana bindÃga.
Labarin Diomande yana nuna mana cewa nasara tana tare da buri, kuma nasara tana tare da juriya, sannan dole sai an sha wahala kafin akai ga nasara, kuma tarihinsa yana nuna cewa "Yaro ɓata hankalin dare ka yi suna" ba a samun ɗaukaka rana ɗaya, ko lokaci ɗaya, sannan hakan yana nuna mana Allah Yakan iya sauya rayuwar bawa cikin ƙanƙanin lokaci, wataƙil a wancan lokacin wasu suna ganin abinda yayi na rubuta sunan Ronaldo a matsayin hauka, wataƙil kuma hakan ne ya zaburar da shi wajen gina mafarkinsa.
Tarihinsa yana nuna mana cewa wani zaiyi nasara a ƙananan shekaru, wani kuma sai ya girma, amma a duk lokacin da aka samu nasara ba'a duba shekarun, Barrack Obama ya zama shugaban Amurka a ƙasa da shekaru 45, a lokacin da Donald Trump ya zama da shekaru 70, dukkaninsu sun yi nasara, amma lokaci ne ya bambanta, komai tsawon lokaci kada ka sare, kokuma kaja da Baya. Sannan wannan yana nuna mana cewa "Ka Gano inda kake da wata baiwa, kuma kayi amfani da ita wajen gina Rayuwarka".
Sannan wannan Ya nuna mana cewa;
Lokacin Da Kayi Nasara: "Ba Lokacin Gane Masoyi Bane"
Lokacin daka cimma nasara ba lokacin gane masoyi bane, lokaci ne da kowa yake zuwa wajenka, yanzu ya zama abin alfahari, duniya ba ta son rago, tana son wanda ya yi nasara ne kawai, kai ma ka tashi ka dage.
Lokacin da kake fafutuka a lokacin da yawa dariya kake ba su, wasu kallon mahaukaci suke yi maka, wasu kuma kallon wahalalle, akwai kuma masu yi maka ganin mai aikin banza kawai.
Ƙalilan ne zasu yi maka fatan alkairi, har ma su yi fatan ka yi nasara.
Yau dai ga mafarkin Diomande ya cika, zai buga kwallon a ƙungiyar da Ronaldo yayi wasa, wataƙil nan gaba shima ya goya number 7 ɗin, wacce Ronaldo ya goya, kuma duk a ƙungiya ɗaya. Ba labari ne na kwana ɗaya ba, akwai wahala, taƙaici, daya jure wanda wataƙil kai Bazaka jure domin gina mafarkinka ba.
Duniya ba ta san rago, ba ta alfahari da rago, ka tashi kayi aiki domin cika mafarkinka.
Za ka iya zama k**ar Diomande ne kaɗai, idan ka yi aiki tuƙuru kuma kayi addu'a.
Allah Ya cika mana mafarkin mu na alkairi.