30/08/2026
Kafin Ka Kushe Gwamnatin Yobe Akan Matsalar Ciwon Koda Ya Kamata Ka San Wannan;
A kalla a kowanne wata mutum 600 ne ake musu wanki koda kyauta sau 2 a sati kamar yanda Gwamnatin Jihar Yobe ta sanar a baya.
Kowanne wankin koda guda 1 anayinsa ne akan kudi N60,000 a asibitin Mallam Aminu Kano (AKTH) ko kuma asibitin horaswa na Maiduguri (UMTH).
Ma'ana ko wanne daga cikin mutum 600 ana masa aikin N120,000 a kowanne sati, a wata kuma ana masa aikin N480,000 a kyauta.
Idan ka hada N480,000 sau 600 ya nuna Gwamnatin Mai Mala Buni tana kashe kudade kimanin Naira Miliyan Dari Biyu da Tamanin da Takwas (N288,000,000) tsakanin biyan kudin wankin koda da kayan aikin.
Gwamnatin Mai Mala Buni ta kashe kudade kimanin Naira Biliyan Biyu (N2B) domin gudanar da bincike akan abunda ke kawo yawaitan ciwon koda a yankin kasar Bade.
Har ila yau Gwamnatin Mai Mala ta kashe kudade kimanin N1B domin kafa cibiyar bincike wanda zata gano inda matsalar yawan ciwon kodan yake.
Duk girman Jihar Borno da yawan ciwon kodan da suke fama dashi wanda Gwamna Zulum yace kimanin mutane 668 ake yiwa wankin koda a kowanne wata amma wajen wankin koda na kyauta guda 1 suke dashi a Specialists Hospital nasu.
Meyasa a Yobe ya zama abun cece-kuce? Muna goyon bayan akafa cibiyar wankin koda a Gashu'a amma fa dole a gode wanda aka samu sai a nemi kari.
Daga Husaini Mohammed Isa