Nguru film factory

Nguru film factory FADAR ANBATON ANNABI MUHAMMADU

04/08/2023

Sarkin sadaukaii dan abdullahi
Annabi muhammad s.a.w.♥️❤️♥️❤️🙋

30/07/2023

Muhammadar rasulillah s a w ❤️❤️💘♥️

25/05/2023
14/05/2023

Masha Allah

24/09/2022

HAKURI 'IRIN NA ANNABI AYYUB.

Allah T yabawa annabi ayyub arziki na dukiya da 'ya'ya maza har 7 da 'ya'ya mata kwatankwacinsu, sai Allah yayi nufin ya jarabci bawansa kuma annabinsa ayyub, sai kasuwancinsa s**a karye, yayansa s**a mutu, gidansa ya rushe, dabbobinsa s**a mutu sannan Allah ya jarabceshi da rashin lafiya ajikinsa.

Lokacin da rashin lafiya ta tsananta gareshi mutane s**a gujeshi don tsoron karsu gogi kalan rashin lafiyan, s**a fitar dashi wajen gari ba wanda yatsaya tareda shi sai matarshi tana masa hidima tana kula dashi, takanje tayi aiki a gidaje don tasamu kudin dazata kula da kanta da mijinta.

Bayan wani lokaci sai mutanen gari s**a kyamaceta tsoron kada su gogi cutan mijinta a jikinta har yakai babu wanda zai dauketa aiki.

Ance annabi ayyuba ya rayu tareda wannan cuta tsawon shekara 18 yana hakuri bai taba kai kuka ga kowa ba, lokacin da matarsa taga yanayi ya tsananta a garesu sai tace, ya annabin Allah ka roki Allah ya yaye maka wannan bala'i, sai yace shekara Nawa mukayi acikin jin dadi? Tace 80, yace inajin kunyar Allah saboda banyi rayuwar da takai na jin dadinaba da Allah yayimin acikin wannan bala'i.

Sai matarsa lokacin data rasa mafita ta yanke shawaran siyar da Rabin gashinta don tasamu abincin da zasuci, lokacin data kawo abincin annabi ayyub ya tambayeta ina tasamu bata fada ba, washe gari ta siyar da gashinta saura takara samo musu abinci s**aci.

Lokacin da kanta ya yaye sai annabi ayyub yaga babu gashi sai ya fahimta meke faruwa, sai yaji kunyan ubangiji kar yaroki shi yabashi lafiya sai yace k**ar yadda Qur'ani yazo dashi.
"ربي إني مسني الضر وأنت أرحم الراحمين"
Ya Allah ni cuta ta sameni kuma Kaine mafi jinkan masu jinkai.

Sai al'amari yazo daga wurin Allah madaukakin sarki cewa, "أركض برجلك هذا مغتسل بارد و شراب"
Ka shuri kasa da kafarka ruwa mai Sanyi zai fito nasha da wanka.

Lokacin da Allah T ya h**e mai wannan ruwa na waraka da yasha yayi wanka sai yatashi garau k**ar bai taba yin cuta ba, sai matarshi ta dawo bata ganeshi ba, ta tambayi mutumin data gani a tsaye awurin ina marar lafiyan dake kwance 'anan? Kana k**a dashi lokacin da yake lafiya lau. Yace baki gane niba? Tace waye kai? Yace nine ayyub.

Ibn Abbas yace 'itama matarshi Allah T ya karramata saboda hakurin da tayi tareda shi aka dawo mata da yarintanta saida ta haifawa annabi ayyub 'ya'ya 26 babu mace aciki Allah T yana cewa acikin alqur'ani.
"وآتيناه أهله و مثلهم
معهم "
Sai muka bashi 'iyalansa da kwatankwacinsa tareda su.

Lokacin dajin dadi yazo ga annabi ayyub sai yayi nufin yacika alqawarin daya dauka akan matarsa nacewa 'idan Allah yabashi lafiya zai mata wani adadin bulala saboda laifi datayi na Neman taimako daga wurin wani na magani don ayi masa, sai Allah T ya tausaya mata ya umurci ayyub da ya cure bulalun adadin dayayi alkawari awuri daya yayi dukan dasu sau daya k**ar yadda Qur'ani yazo dashi.
وخذ بيدك ضغثا فاضرب به ولا تحنث

Allah T yayi yabo ga hakurin da annabi ayyub ya nuna acikin alqur'ani yace, mun sameshi mai hakuri madalla da wannan bawa shi mai maida al'amari ne zuwa ga Allah.

Abin lura daga kissar annabi ayyub shine, lokacin da bala'i yakai maka kololuwa katuna da annabin Allah ayyub kayi hakuri kasani cewa hakurinka a tekun hakurin annabi ayyub k**ar digon ruwa ne, kuma dukda shi annabi ne yafika kusanci da soyuwa awurin Allah amma an jarabceshi da bala'in dayafi naka.

Ya Allah kasa mudace duniya da lahira kuma muci jarabawoyin rayuwa.

Katura Zuwa Group 3 Kachal Domin Al'umma Su Amfana ❤️

26/08/2022

F K D production

14/08/2022

Address

Street Adamu Chiroma
Nguru
213

Telephone

+2348036945369

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nguru film factory posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share