Voice Of Nguru

Voice Of Nguru Your trusted source for real stories, news, and voices from Nguru town.

‎AL’UMMAR NGURU NA CIGABA DA FAMA DA RASHIN WUTA‎‎Akwai masu faɗa a ji da za su iya ɗaukar waya su kira sau ɗaya kawai, ...
23/08/2026

‎AL’UMMAR NGURU NA CIGABA DA FAMA DA RASHIN WUTA

‎Akwai masu faɗa a ji da za su iya ɗaukar waya su kira sau ɗaya kawai, kuma hakan na iya taimakawa wajen magance irin wannan matsalar da al’ummar garin Nguru ke fuskanta a yanzu.

‎Matsalar wutar lantarki ta yi yawa, abin takaici kuma ana ganin kamar akwai rashin kulawa daga wasu masu faɗa a ji a cikin gari. Ban sani ba ko hakan yana da alaƙa da rashin sanin halin da ake ciki, musamman ganin cewa wasu daga cikinsu suna da Solar a gidajensu.

‎Amma abin da ke faruwa yanzu ba ƙaramin abu ba ne. Rashin wutar lantarki ya jefa al’umma cikin matsala, har ana ganin mutane suna ta yawon neman ruwan sha saboda rashin wutar da za ta taimaka wajen samar da shi. Gaskiya abin ba daɗi ne.

‎Waɗanda suke kusa da masu faɗa a ji, muna roƙonku da ku isar musu da halin da al’ummar Nguru suke ciki. Akwai buƙatar a ɗauki mataki cikin gaggawa domin rage wannan matsala.

‎Allah Ya kawo mana sauƙi, Ya kyauta.

18/08/2026

Me ya sa sai lokacin zaɓe ne matasan Nguru suke yawan kafa ƙungiyoyin siyasa, amma lokacin da al’umma ke fuskantar matsala ba a ganin irin wannan haɗin kai?

‎A lokacin da Nguru ke fuskantar ƙalubale rashin ayyukan yi, matsalar ilimi, rashin isassun abubuwan more rayuwa da sauran matsalolin al’umma—ina muryar matasa take?

‎Shin ba za mu iya haɗa kai mu kafa ƙungiyoyin matasa domin neman mafita tun kafin lokacin zaɓe ba?

‎Siyasa tana zuwa ne lokaci-lokaci, amma matsalolin Nguru suna nan kullum.

‎Ya kamata matasa su zama masu neman canji, ba kawai masu fitowa lokacin da ake neman kuri’a ba.

‎Tambaya ita ce: Shin matasan Nguru suna shiga siyasa ne domin canza al’umma, ko kuma domin biyan bukatun ’yan siyasa?

SANARWA GA ƊAUKACIN AL’UMMAR NGURU‎‎MAULUDIN ZAWIYYAR MAULANA SHEIKH MUHAMMADU NGIBIRIMA ZULMA ARIF (R.A.)‎‎An sanar da ...
16/08/2026

SANARWA GA ƊAUKACIN AL’UMMAR NGURU

‎MAULUDIN ZAWIYYAR MAULANA SHEIKH MUHAMMADU NGIBIRIMA ZULMA ARIF (R.A.)

‎An sanar da ɗaukacin al’ummar Nguru da maƙwabta cewa, da izinin Allah, za a gudanar da Zaman Mauludin Zawiyyar Maulana Sheikh Muhammadu Ngibirima Zulma Arif (R.A.), a Nguru.

‎Ranar Litinin, 24/08/2026
‎11/03/1448H, in shā Allah.

‎Wannan babban taro na addini na daga cikin abubuwan da ke haɗa al’ummar Nguru da sauran Musulmi daga wurare daban-daban domin tunawa, wa’azi da ƙara soyayyar Manzon Allah ﷺ.

‎Muna roƙon Allah Ya kai mu wannan rana cikin ƙoshin lafiya da aminci, Ya kawo baƙi da masu halarta cikin aminci, Ya ba mu ikon kammala Mauludin lafiya, cikin zaman lafiya da albarka.

‎Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya ƙara mana soyayyar Manzon Allah ﷺ. Amin.

‎Voice of Nguru

15/08/2026

NGURU GARIN AL’BARKA

‎Nguru, garin Allah!
‎Nguru, garin malamai!
‎Nguru, garin kasuwanci!
‎Nguru, garin ilimi!
‎Nguru, garin arziki!
‎Nguru, garin kyawawan mata!

‎Nguru ba gari ba ne kawai gari ne mai tarihi, al’adu, ilimi da mutanen kirki.
‎Gari ne da ke alfahari da malamai, ’yan kasuwa, manoma, matasa da manyan mutane masu tasiri.

‎Nguru garinmu, alfaharinmu!

TAIMAKO GA WASU IYALAI A BULABULIN WARD, NGURUGa wasu iyalai da ke zaune a Bulabulin Ward, cikin Garin Nguru, waɗanda su...
14/08/2026

TAIMAKO GA WASU IYALAI A BULABULIN WARD, NGURU

Ga wasu iyalai da ke zaune a Bulabulin Ward, cikin Garin Nguru, waɗanda suke cikin mawuyacin hali sakamakon matsin rayuwa da kuma rashin ingantaccen muhalli.

Idan ruwan sama ya sauko da dare, iyalan kan shiga cikin wani yanayi mai matuƙar wahala, inda suke kwana a zaune saboda rashin isasshen wurin kwanciya da kuma rashin matsuguni mai kyau.

A halin yanzu, suna neman taimakon al’umma wajen samun sabon ɗakin bukka ko wani matsuguni da zai ba su damar samun wurin kwanciya da kuma sauƙaƙa musu wannan mawuyacin hali da suke ciki.

Muna kira ga masu hali, ’yan kasuwa, ƙungiyoyin agaji da sauran masu kishin al’umma da su taimaka wa wannan iyali gwargwadon iko.

Duk wanda ke son ƙarin bayani ko kuma yana son taimakawa kai tsaye, zai iya tuntuɓar wakilinsu:

Mal. Audu Baba: 0806 958 0413

Allah Ya saka wa duk wanda ya taimaka da alheri, Ya kuma sauƙaƙa musu halin da suke ciki.

Voice of Nguru Muryar Al’umma.

WAQAFI KO SADAQATUL JARIYA‎‎Al’ummar garin Kaigamari, da ke yamma da Afunori, Nguru Local Government Area, Yobe State, n...
14/08/2026

WAQAFI KO SADAQATUL JARIYA

‎Al’ummar garin Kaigamari, da ke yamma da Afunori, Nguru Local Government Area, Yobe State, na matukar bukatar masallaci.

‎A halin yanzu, masallacin da suke amfani da shi yana cikin yanayi mai hatsari, domin suna fargabar cewa zai iya rugujewa a kowane lokaci. Saboda haka, suna tilasta yin Sallah a waje. Idan kuma aka samu ruwan sama, kowa kan koma gidansa domin yin Sallah.

‎Wannan kira ne ga duk wani musulmi da Allah Ya azurta, musamman masu sha’awar Waƙafi ko Sadakatul Jariya, da su dubi wannan hali tare da taimakawa wajen gina masallaci ga al’ummar Kaigamari.

‎Gina masallaci babban aikin alheri ne, kuma taimakawa wajen samar da wurin ibada na daga cikin ayyukan da ake fatan samun lada mai dorewa.

‎Allah Ya sanya a dace, Ya ba mu ikon taimakon addinin Musulunci, Ya kuma saka wa duk wanda zai bayar da gudummawa da mafificin alheri.

12/08/2026

1. A matsayinka na matashi ɗan Najeriya, kana ganin wannan tsarin mulki yana ba matasa damar taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙasar nan, ko kuwa an bar matasa a baya?

‎2. Me ya sa matasa da suke da ƙarfi, ilimi da basirar kawo sauyi basa samun isasshen dama a harkokin mulki, tattalin arziki da ci gaban al’umma?

‎3. A wannan Ranar Matasa ta Duniya, wane irin sauyi kake son gani ga matasan Najeriya, musamman matasan Nguru, domin su samu dama su gina rayuwarsu da makomar ƙasar nan?

KIRA GA GWAMNATIN YOBE DA GWAMNATIN ƘARAMAR HUKUMAR NGURUMuna kira ga Gwamnatin Jihar Yobe da Gwamnatin Ƙaramar Hukumar ...
12/08/2026

KIRA GA GWAMNATIN YOBE DA GWAMNATIN ƘARAMAR HUKUMAR NGURU

Muna kira ga Gwamnatin Jihar Yobe da Gwamnatin Ƙaramar Hukumar Nguru da su gaggauta duba halin da al’ummar da ke zaune a unguwar Tsohuwar Health Tech da yankin Jingan Kamilu suke ciki.

Al’ummar waɗannan yankuna suna cikin matsanancin hali sakamakon ambaliyar ruwa da ruwan sama mai ƙarfi da aka samu a daren jiya a garin Nguru.

Muna roƙon gwamnati da hukumomin da abin ya shafa su kai ɗaukin gaggawa ga waɗanda wannan iftila’i ya shafa, domin rage musu wahala da kare rayuka da dukiyoyi.

Haka kuma, muna kira ga masu hannu da shuni, ‘yan kasuwa da manyan ‘yan siyasa da su taimaka wa waɗanda wannan iftila’i ya shafa.

Allah Ya kawo mana sauƙi, Ya kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Nguru. Ameen.

SANARWA GA IYAYEN NGURU‎‎Dignity Protection Team, Nguru, Yobe State na gudanar da wani shiri na musamman na karin darasi...
11/08/2026

SANARWA GA IYAYEN NGURU

‎Dignity Protection Team, Nguru, Yobe State na gudanar da wani shiri na musamman na karin darasin kyauta da darussan tarbiyya (moral lesson) ga yara, domin taimaka musu wajen inganta karatunsu da shirya su domin samun kyakkyawar makoma.

‎Shirin zai gudana ne a Alhamis, 13 ga Agusta, 2026, daga ƙarfe 4:30 na yamma zuwa 5:30 na yamma, a Hausari Primary School, Nguru, Yobe State.

‎Wannan wata dama ce mai matukar amfani ga iyaye da yara. Saboda haka, muna kira ga iyaye da masu kula da yara da su yi ƙoƙari su tura yaransu domin su amfana da wannan gagarumin shiri na ilimi da tarbiyya kyauta.

‎Muna yabawa Dignity Protection Team bisa wannan kyakkyawan kokari na tallafa wa ilimin yara da gina kyakkyawar makoma ga al’ummar Nguru.

‎Voice of Nguru na kira ga iyaye: Kada ku bari yaranku su rasa wannan dama.

‎Domin karin bayani: 08103545453 / 07025839521

‎Voice of Nguru Muryar Al’umma.

MUSA MUHAMMAD NURA YA BAYAR DA KYAUTAR FILIN MAKABARTA A NGURUMusa Muhammad Nura (Ɗan Iyan Nguru), ya bayar da kyautar f...
11/08/2026

MUSA MUHAMMAD NURA YA BAYAR DA KYAUTAR FILIN MAKABARTA A NGURU

Musa Muhammad Nura (Ɗan Iyan Nguru), ya bayar da kyautar fili mai girman Hekta 4 domin samar da makabarta a yankin hanyar Machina, yammacin Mai Mala Quarters, Nguru.

Musa Muhammad Nura ya mika takardun filayen ga Mai Martaba Sarkin Nguru, Alh. Mai Mustapha Ibn Kyari, domin fara shirye-shiryen samar da makabartar.

Wannan kyauta ta zo a daidai lokacin da garin Nguru ke kara fadada zuwa wannan yanki, inda ake samun sabbin gidaje da cibiyoyi kamar FMC, Nayi-Nawa, Mala Quarters da Madinatul Shehu Fatihu.

Muna roƙon Allah Ya saka wa Musa Muhammad Nura da alheri, Ya albarkaci wannan sadaka, kuma Ya sanya ta zama Sadakatul Jariya mai ci gaba da samun lada.

Allah Ya saka da alheri.

Address

Ngurum

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Voice Of Nguru posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share