05/11/2025
SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR NINGI YA SAYI FILI DOMIN BUNKASA KASUWAR HASTI DA DABBOBI TARE DA KADDAMAR DA GININ SHAGUNA.
A kokarinsa na bunkasa harkokin noma da tattalin arziki, shugaban karamar hukumar Ningi, Hon. Nasiru Zakaria Dankasuwa, ya sayi filaye tare da kaddamar da ginin shagunan kasuwanci a babban kasuwar Ningi.
Shugaban ya bayyana cewa ya sayi fili mai darajar naira miliyan goma sha biyu (₦12,000,000) a unguwar Sabuwar Tiffi domin gina kasuwar dabbobi da hatsi. Ya ce dukkan nau’ukan kayan amfanin gona da dabbobi irin su shanu, tumaki da awaki za su sami matsuguni a sabon kasuwar dabbobi da hatsi ta Ningi da za a bude nan gaba kadan.
Hakazalika, Hon. Dankasuwa ya kaddamar da ginin sabbin shaguna goma a babban kasuwar Ningi domin inganta harkokin kasuwanci da ci gaban tattalin arziki a yankin.
Shugaban ya yi kira ga al’ummar ‘yan kasuwa da masu sana’o’i da su ci gaba da baiwa gwamnatin jihar da ta karamar hukuma goyon baya domin kara inganta tattalin arziki da samar da ayyukan yi, wanda zai kara bunkasa cigaban bil’adama.
A jawabinsa na godiya, a madadin shugaban kasuwa, Alhaji Naduni Ningi, ya tuna cewa a baya-bayan nan shugaban ya gudanar da muhimman ayyuka da s**a inganta harkokin kasuwanci, ciki har da samar da wutar lantarki ta solar a kasuwannin Ningi da Gadar Maiwa. Haka kuma ya gode masa bisa sayen filaye na dindindin domin kasuwannin Jimi, Gadar Maiwa da Masuss**a.
Shugaban kasuwa ya kuma roki ‘yan kasuwa da al’ummar masu sana’a da su ci gaba da baiwa shugaban karamar hukumar hadin kai domin kara bunkasa tattalin arziki a karamar hukuma da jihar baki daya.
Kamilu Barau
Jami’in Yaɗa labarai na karamar hukumar Ningi.