Burra Update

Burra Update Burra Update | Muryar Al'ummar Burra
Muna kawo sahihan labarai, ilimi, wasanni, sanarwa da abubuwan ci gaban al'umma cikin gaskiya da adalci.

14/07/2026

ABUN Mamaki Baya Karewa Kalli kaga 🤔🤔🤔

14/07/2026

BIDIYO: Yadda matan zumunta s**a tarbi sanannen malamin addinin Musulunci, kuma ɗan takarar gwamnan jihar Gombe a zaɓen shekarar 2027 ƙarƙashin jam'iyyar PDP, Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami a waƙa wanda babu kiɗa a ciki, yayin da ya kai ziyarar jaje a majami'ar ECWA da ke Federal Low-cost a garin Gombe.

Abun tausayi 😥 “Na auri matata daga gida mai ƙaramin ƙarfi, na kai ta Burtaniya a shekarar 1970, kuma na riƙa kashe fam ...
14/07/2026

Abun tausayi 😥 “Na auri matata daga gida mai ƙaramin ƙarfi, na kai ta Burtaniya a shekarar 1970, kuma na riƙa kashe fam £11,000 a kowace shekara wajen ɗaukar nauyin karatunta har ta kai matakin digirin digirgir (PhD).
......Amma da ta kammala karatu kuma ta samu kafuwa, sai ta kai ni ƙara a kotu a Burtaniya, tana zargin ƙarya cewa na yi wa ’yata mai shekara 11 fyade, domin a kore ni daga ƙasar.”
____________________

Wannan shi ne labarin wani ɗan Najeriya, wanda cikin hawaye ya ce matarsa ta kore shi daga rayuwarta tare da raba shi da ‘ya’yansu bayan ya sadaukar da dukiyarsa da ƙoƙarinsa wajen tabbatar da ta samu ilimi har ta kai matakin PhD a Burtaniya.

Wannan duniya, Ina zaki damu??

08/07/2026

Allah Ya Rufa Asiri 😭😭
Burra Update

‎DA DUMI-DUMI: Ana Hasashen Malam Nasiru El-Rufai Zai Janye Goyon Bayansa Daga Jam'iyyar  ADC, an sami wasu kwafin takar...
06/07/2026

‎DA DUMI-DUMI: Ana Hasashen Malam Nasiru El-Rufai Zai Janye Goyon Bayansa Daga Jam'iyyar ADC, an sami wasu kwafin takardu na wasika da Malam Nasiru El-rufai ya aika ga Uwar jam'iyyar.

‎Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, na iya janye goyon bayansa ga Jam’iyyar ADC.

‎A cewar majiyar, wannan na da alaƙa da zargin cewa jam’iyyar ta nuna halin ko-in-kula game da halin da El-Rufai ke ciki bayan da hukumomin tsaro s**a tsare shi.

‎Haka kuma, a jiya wata murya ta bazu a kafafen sada zumunta, wadda ake zargin ta ɗan takarar gwamnan Jihar Kaduna na ADC, Isah Ashiru Kudan, ce. A cikin muryar, an ji ana caccakar El-Rufai, inda aka ce ba mutumin kirki ba ne, tare da ikirarin cewa shiga ADC da ya yi saboda neman tikitin takara ne kawai, ba wai don goyon bayan El-Rufai ko siyasar da yake tafiya a kanta ba.

‎Sai dai, har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, ba a tabbatar da sahihancin muryar ba, kuma babu wata sanarwa a hukumance daga El-Rufai, Isah Ashiru Kudan ko shugabannin ADC da ta tabbatar da waɗannan zarge-zarge.

Yanzu-yanzu;Rahotanni na cewa hukumar EFCC ta gano dala biliyan 5, takardun da ake zargin an riga an rubuta sak**akon za...
04/07/2026

Yanzu-yanzu;
Rahotanni na cewa hukumar EFCC ta gano dala biliyan 5, takardun da ake zargin an riga an rubuta sak**akon zaɓen 2027, sarƙoƙin zinari da darajarsu ta kai naira tiriliyan ₦1, da kuma motocin alfarma 200 a gidan tsohon gwamnan Jihar Abia, T. A. Orji, bayan samame da ta kai.

Ana kuma zargin ya ƙi amsa gayyatar EFCC sau da dama kuma ya ɓuya na tsawon watanni. Idan waɗannan zarge-zarge s**a tabbata, wannan wani babban abin takaici ne ga kasa irin ta Najeriya.

'Yan siyasar Najeriya da mugun cin hanci sun jefa al'umma cikin talauci, yayin da suke tara dukiyar da ba ta dace ba. Doka ta yi aikinta ba tare da nuna bambanci ba.

— Daily Nigerian

Abun da Jami'an Tsaron Nigeria s**a iya kenan 🤓🤓🤓'Yan sanda sun ci gaba da kamen Motoci marasa Lamba da wadda aka ɓoye a...
03/07/2026

Abun da Jami'an Tsaron Nigeria s**a iya kenan 🤓🤓🤓
'Yan sanda sun ci gaba da kamen Motoci marasa Lamba da wadda aka ɓoye a Katsina

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Katsina ta bayyana cewa ta ci gaba da k**a motocin da ke yawo ba tare da lambar rajista ba, da waɗanda aka rufe lambobinsu, ko kuma waɗanda lambobinsu s**a lalace har ba a iya ganewa.

Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Jihar, DSP Abubakar Aliyu Sadiq ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a, 3 ga Yuli, 2026.

Ya ce an ɗauki wannan mataki ne a wani ɓangare na ƙoƙarin rundunar na ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al'umma, tare da tabbatar da cewa ana bin dokokin zirga-zirga da tsaro a faɗin jihar.

Idan kasan kana da Asusun banki Wanan Post din naka NE🤔🤔BABBAN BANKIN NIGERIA TA SOKE LASISIN WASU BANKUNA 46.Babban Ban...
02/07/2026

Idan kasan kana da Asusun banki
Wanan Post din naka NE🤔🤔
BABBAN BANKIN NIGERIA TA SOKE LASISIN WASU BANKUNA 46.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke lasisin gudanar da harkokin bankunan Microfinance 46 a Fadin Kasar nan, a cewar Babban Bankin, matakin ya fara aiki daga yau Laraba 1 ga wannan Wata ta Yuli, 2026.

CBN ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne saboda bankunan sun kasa cika ƙa'idojin da Dokar Banks and Other Financial Institutions Act (BOFIA) a Turance ta tanada.

A cewar bankin, wasu daga cikin bankunan ba su da isassun kadarori da za su biya basuss**a, wasu sun rufe ayyukansu ba tare da amincewar Babban Bankin ba, wasu sun daina aiki na tsawon lokaci, wasu kuma ba su fara aiki cikin wa'adin da aka gindaya ba ko kuma sun gaza cika mafi ƙarancin jarin da doka ta tanada.

CBN ta ce matakin na da nufin kare zaman lafiyar tsarin kuɗi na ƙasa, tabbatar da kariyar ajiyar kwastomomi, da kuma ƙarfafa amincewar jama'a da tsarin bankunan Najeriya.

BATV BAUCHI.

30/06/2026

Ga Wani Sako Mai Muhimanci,
Wanda Jama'a zasu anfana sosai

Menene Gaskiyar Magana Akan Mutuwaar Musa Me Sana'a danaga ana yadawaa ?🤔😭🤣🤔😭
30/06/2026

Menene Gaskiyar Magana Akan Mutuwaar Musa Me Sana'a danaga ana yadawaa ?🤔😭🤣🤔😭

Address

Burra Update Ningi LGA
Ningi
742102

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Burra Update posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share