09/11/2025
Kungiyar JIBWIS ta mayar da martani kan zargin “Kisan Kiristoci” da ya janyo takaddama tsakanin Najeriya da Amurka
Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, ta bayyana damuwa kan takaddamar diflomasiyya da ke tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriya da gwamnatin Amurka, sak**akon rahotanni marasa tushe da s**a zargi Najeriya da aiwatar da abin da aka kira “kisan Kiristoci” a kasar.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Talata, 4 ga Nuwamba, 2025, JIBWIS ta bayyana cewa wannan zargi ba gaskiya ba ne kuma yana iya rura wutar rikici, tana mai jaddada cewa matsalolin tsaro da ake fuskanta a Najeriya irin su ta’addanci, garkuwa da mutane, da rikice-rikicen al’umma ba su da tushe daga addini, illa dai matsalolin tattalin arziki, cin hanci, da raunin tsarin mulki.
Kungiyar ta jaddada cewa Musulmai da Kiristoci duka sun kasance cikin wadanda s**a fi fuskantar tasirin wadannan matsaloli, inda ta ce kiran abin da ke faruwa “kisan Kiristoci” bai inganta ba kuma yana barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
JIBWIS ta kuma yi kira ga kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) da sauran shugabannin addinin Kirista da su nesanta kansu daga irin wadannan zarge-zargen, tare da bayyana cewa dukkan shugabannin addinai a kasar suna da alhakin tabbatar da gaskiya da kuma guje wa amfani da addini wajen cimma manufar siyasa ko ta kasashen waje.
Kungiyar ta shawarci gwamnatin Amurka da ta yi la’akari da bincike na gaskiya da hujjoji kafin daukar matakai, tare da mutunta ikon Najeriya da kare martabar hadin kan kasar. Ta kuma bukaci Amurka da ta mayar da hankali kan bunkasa zaman lafiya, yaki da ta’addanci, da inganta tsaro, maimakon wani bangare.
Haka zalika, JIBWIS ta shawarci kungiyoyin farar hula, masu sa ido kan hakkin dan Adam, da cibiyoyin bincike su kasance masu rahotanni na gaskiya da hujja, saboda wallafa alkaluma marasa tushe na iya haifar da rikici da rashin fahimtar juna. Ta kuma yi kira ga ’yan jarida da masu amfani da kafafen sada zumunta da su guji yada labarai marasa inganci da kalmomin da ke tayar da hankali, domin bin diddigin gaskiya.
Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, wanda ya sanya hannu kan sanarwar, ya mika ta’aziyya ga Musulmai da Kiristocin da s**a rasa ‘yan uwansu ko dukiyoyinsu sak**akon matsalolin tsaro a fadin kasar, yana rokon Allah Ya basu hakuri.
A karshe, JIBWIS ta yaba da diflomasiyyar gwamnatin tarayya wajen shawo kan wannan batu, tare da kira ga ci gaba da hulda ta diflomasiyya da tattaunawa tsakanin Najeriya da Amurka. Kungiyar ta sake jaddada kudirinta na gaskiya, zaman lafiya, da hadin kai tsakanin addinai, tana mai kira ga ’yan Najeriya su kasance masu juriya, kishin kasa, da fata mai kyau a yayin fuskantar kalubalen kasa.
Signed: Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau
National Chairman Jibwis Nigeria
Jibwis Nigeria