Nigeria News update

Nigeria News update 📢 Sharing real-time updates and breaking news from Nigeria. Stay informed, stay ahead. 🇳🇬

A Daina Karɓo Bashi Haka Barkatai – Atiku ya Caccaki Sabon Bashin Gwamnatin TinubuTsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku...
25/04/2026

A Daina Karɓo Bashi Haka Barkatai – Atiku ya Caccaki Sabon Bashin Gwamnatin Tinubu

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar s**a kan manufofin karɓo bashi na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin ta gabatar wa Majalisar Dattawa bukatar amincewa da sabon bashi na waje dala miliyan 516 ($516m), wanda ya kai kusan naira biliyan 700 da ɗan ƙari.

Atiku ya bayyana wannan mataki a matsayin rashin kishin ƙasa, yana mai cewa hakan na iya jefa Najeriya cikin matsin tattalin arziki mai tsanani.

Ya kuma gargaɗi gwamnati da ta guji ci gaba da karɓo bashi ba tare da cikakken shiri na yadda za a biya ba, yana mai cewa hakan na ƙara jefa ‘yan ƙasa cikin wahala.

Bugu da ƙari, Atiku ya nuna damuwa cewa yawaitar bashi na iya sa masu zuba jari na ƙasashen waje su rasa ƙwarin gwiwa ga tattalin arzikin Najeriya.

NA MUSAMMAN: Oluremi Tinubu Ta Ƙaddamar Da Shirin ECoN A Kano, Ta Bukaci Mayar Da Hankali Kan Masana’antuDaga Ma’aikatar...
25/04/2026

NA MUSAMMAN: Oluremi Tinubu Ta Ƙaddamar Da Shirin ECoN A Kano, Ta Bukaci Mayar Da Hankali Kan Masana’antu

Daga Ma’aikatar Yaɗa Labarai

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da wani sabon shiri mai taken “Energise Commercialisation Now” (ECoN) a birnin Kano ranar Alhamis, inda ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su daina tsayawa ga tunanin ayyuka kawai, maimakon haka su duƙufa wajen gina masana’antu.

Da take jawabi a wajen taron, Sanata Oluremi ta bayyana cewa Nijeriya ƙasa ce mai cike da fasaha da hazaka, inda kullum ake samun sabbin ra’ayoyi daga jami’oi da cibiyoyin fasaha, amma abin takaicin shi ne yawancin waɗannan ra’ayoyin ba sa komawa ayyukan da za su amfani al’umma a aikace.

Manufar shirin ECoN

Uwargidan Shugaban Ƙasar ta ce: “Wannan shiri na ECoN wani gagarumin mataki ne na dinke barakar da ke tsakanin tunanin ayyuka da aiwatar da su. Muna son samar da yanayi inda za a tallafa wa ra’ayoyin matasa da masu bincike domin su zama manyan masana’antu.”

Ta ƙara da cewa shirin zai taimaka kwarai wajen samar da ayyukan yi, bunƙasa tattalin arziki, da kuma sanya Nijeriya takara da sauran ƙasashen duniya a fagen kasuwanci da fasaha. Ta kuma nanata cewa mata da matasa ne za su kasance a gaba-gaba a dukkan shirye-shiryen gwamnati.

A nasa jawabin, Ministan Fasaha da Kimiyya, Dr. Kingsley Udeh, ya ce an samar da ECoN ne domin magance tsohuwar matsalar nan ta Nijeriya, inda ake bincike mai kyau amma ba a kai shi kasuwa domin ya zama kuɗi.

A cewarsa, bincike da dama na nan sun maƙale a dakunan gwaje-gwaje (laboratories) saboda rashin kuɗi ko kuma rashin hanyar kai su ga masu saye.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna jin daɗinsa kan yadda aka zaɓi Kano domin ƙaddamar da wannan shiri na ƙasa da kuma na shiyyar Arewa maso Yamma. Ya bayyana cewa Kano ta riga ta fara shiri ta hanyar inganta ilimin kimiyya da fasaha da kuma faɗaɗa hanyoyin sadarwa na zamani (ICT).

Shi ma Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, wanda ya yi magana a madadin Gwamnonin

“Dole Mu Ƙera Abubuwan da muke amfani da su a gida Najeriya” — DangoteAttajirin ɗan kasuwa, Aliko Dangote, ya jaddada ce...
25/04/2026

“Dole Mu Ƙera Abubuwan da muke amfani da su a gida Najeriya” — Dangote

Attajirin ɗan kasuwa, Aliko Dangote, ya jaddada cewa dole ne Najeriya ta fara ƙerawa da ƙirƙira kayayyakin da take amfani da su, tare da gina ingantaccen tsarin wutar lantarki domin bunƙasa tattalin arziki.

Dangote ya ce dogaro da shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje na hana ci gaban masana’antu, yana mai cewa lokaci ya yi da za a mayar da hankali kan samar da kayayyaki a cikin gida.

Ya kuma ƙara da cewa ingantaccen tsarin wutar lantarki (power grid) na da matuƙar muhimmanci wajen tallafawa masana’antu da rage tsadar samar da kayayyaki.

A cewarsa, idan aka haɗa ƙoƙarin gwamnati da masu zaman kansu, Najeriya za ta iya kaiwa ga samun cikakken ci gaba a fannoni k**ar masana’antu, mak**ashi da tattalin arziki gaba ɗaya.

Da ɗumi-ɗumi: Maganar Amurka na shirin ɗaukar mataki kan Gbajabiamila kan Yunkurin wargaza jam’iyyar ADC –An kai ƙorafi....
25/04/2026

Da ɗumi-ɗumi: Maganar Amurka na shirin ɗaukar mataki kan Gbajabiamila kan Yunkurin wargaza jam’iyyar ADC –An kai ƙorafi.

Maganar da Femi Gbajabiamila ya yi na cewa a “zauna a cikin jam’iyya a wargaza ta” ta jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasar Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon Kakakin Majalisar Wakilai kuma shugaban ma’aikatan fadar Gwamnatin Tarayya ya faɗi hakan ne yayin wani taro a Abuja, inda ya ƙarfafa Leke Abejide da ya ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) domin “yakarsu daga ciki”.

Wannan furuci ya tayar da kura sosai, inda wasu ‘yan siyasa da masu sharhi ke ganin hakan na iya zama yunƙurin katsalandan cikin harkokin jam’iyyar adawa.

A wani sabon salo, wani ɗan gwagwarmayar siyasa, Timi Frank, ya rubuta ƙorafi zuwa ga Amurka, yana mai kira da a binciki Gbajabiamila tare da ɗaukar matakan ladabtarwa a kansa.

Ana sa ran gwamnatin Amurka karkashin jagorancin Shugaban Donald Trump ta mayar da martani kan wannan batu na zargin wargaza jam’iyyar adawa ta ADC a Najeriya

Lamarin na ci gaba da ɗaukar hankali, yayin da ake ta muhawara kan yadda ya dace shugabanni su rika mu’amala da jam’iyyun adawa a tsarin dimokuraɗiyya.

Saudiyya Na Neman Haɗin Gwiwa Da Babban Birnin Tarayya Wajen Musayar Kwarewa Kan Cigaban Birane Don Bunƙasa Birnin Abuja...
25/04/2026

Saudiyya Na Neman Haɗin Gwiwa Da Babban Birnin Tarayya Wajen Musayar Kwarewa Kan Cigaban Birane Don Bunƙasa Birnin Abuja

Jakadan Saudiyya a Najeriya, Yousef bin Mohammed Al-Balawi, ya bayyana aniyar ƙasarsa na yin haɗin gwiwa da Babban Birnin Tarayya (FCT) a fannoni k**ar tsaro, tattalin arziƙi da bunƙasa birni mai tsari.

Jakadan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai wa Ministan FCT, Nyesom Wike, a Abuja.

Ya yabawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan sauye-sauyen da ake yi a Abuja, yana mai cewa birnin na ƙara zama mai kyau da tsari.

Al-Balawi ya kuma ce Saudiyya na sha’awar ƙarfafa alaƙa tsakanin FCT da Riyadh, tare da musayar ƙwarewa kan ci gaban birane.

A nasa ɓangaren, Wike ya ce FCT za ta yi amfani da kyakkyawar dangantaka da Saudiyya domin amfanin yankin, yana mai jaddada cewa gwamnatin Tinubu na ƙoƙarin mayar da Abuja birni na zamani mai gogayya da sauran biranen duniya.

Hukumar DSS ta gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Elrufai bisa zargin kutse a wayar Nuhu Ribado.
25/04/2026

Hukumar DSS ta gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Elrufai bisa zargin kutse a wayar Nuhu Ribado.


Da ɗumi-ɗumi:  Yanzu haka matan nan za su saka Pant dauke da Hoton Gwamna: wannan shine Zolayar sa Jaridun turanci suke ...
25/04/2026

Da ɗumi-ɗumi: Yanzu haka matan nan za su saka Pant dauke da Hoton Gwamna: wannan shine Zolayar sa Jaridun turanci suke wa Gwamna Abba da hoton mata dauke da ɗankanfai.

Jaridun kudu na turanci suna buga Labarin Yadda Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta raba 'yan kanfai Pant Amatsayin tallafi ga mata Zawarawa a jihar kano.

Haryanzu dai gwamnatin jihar kano bata ƙaryata labarin ba lamarin da wasu ke kallon labarin Amatsayin Gaskiya.

Masu sharhi na gani wannan rashin kunya ne mata su rike Pant mai dauke da hoton Gwamna a hannu Amatsayin oyoyon da za suyi wa matar shugaban kasa a lokacin data ziyararci jihar kano

Wasu a sashin Sharshi na tambaya shin yanzu haka mata za su saka wannan dankanfai dauke da Hoton Gwamna?

'YAN NIGERIA SUNA JI KUMA SUNA GANI.. Hukumar EFCC ta ayyana neman tsohon Gwamnan jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello ruwa a ...
24/04/2026

'YAN NIGERIA SUNA JI KUMA SUNA GANI..

Hukumar EFCC ta ayyana neman tsohon Gwamnan jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello ruwa a jallo saboda ana zargin ya saci kudin da sun haura Naira Biliyon dari biyu

Jami'an EFCC sun kai farmaki domin su k**a Yahaya Bello amma abin ya gagara, yaki amsa gayyatarsu da gayyatar Kotu, daga karshe dai ya shiga hannu kuma aka bada belinsa ba tare da bata lokaci ba saboda yana jam'iyyar APC

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai baya Kasar da yaji labarin an kulla masa sai ya dawo Kasar, da s**a nemeshi sai ya kai kansa, tuhumar da ake masa bai kai ko rabin kwatan tuhumar da ake yiwa Yahaya Bello ba

Amma abin takaici an hana a bada belin Malam Nasir El-Rufai saboda ya kasance a cikin jam'iyyar 'yan adawa na ADC

Ba shakka an koya wa 'yan Nigeria wani al'amari wanda ba mai kyau ba, ina jiye wa makomar hukumomin da s**a bari 'yan Demokaradiyya na amfani dasu wajen yakar 'yan adawa idan aka wayi gari mulki da karfin iko ya dawo hannun 'yan adawa

Yiwa kowa adalci wajibi ne, da adalci ne ake samun zaman lafiya, kuma a hadu da taimakon Allah cikin kowani yanayi

Yaa Allah Ka bawa Malam Nasir El-Rufai mafita na alheri

2027: Magoya bayan Obi da Kwankwaso sun kafa ƙungiyar yaƙin neman zaɓen suMagoya bayan tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi...
24/04/2026

2027: Magoya bayan Obi da Kwankwaso sun kafa ƙungiyar yaƙin neman zaɓen su

Magoya bayan tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, sun ƙaddamar da wata sabuwar ƙungiyar mai suna Obi–Kwankwaso Movement (OK Movement) a Abuja, domin ƙarfafa haɗin kai kafin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar ADC.

Jaridar PUNCH ta rawaito mai magana da yawun ƙungiyar, Justin Ijeh, ya ce ƙungiyar ta haɗa mambobi daga Obidient Movement, Kwankwasiyya, NNPP da ADC, kuma ta riga ta kafa shugabanci a duk jihohin ƙasar nan da babban birnin tarayya.

Ya bayyana cewa ƙungiyar na da burin kawo sauyi da haɗin kai a ƙasa, tare da jaddada cewa tana adawa da siyasar rarrabuwar kawuna.

Haka kuma, jami’an Obidient Movement sun tabbatar da cewa suna aiki tare da sabuwar ƙungiyar domin cimma tikitin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin ADC.

Samuwar ƙungiyar na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar takaddama a cikin ADC, musamman bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara ba tare da janyewa ga kowa ba.

Sauran jiga-jigan da ake hasashen za su nemi tikitin ADC sun haɗa da Rotimi Amaechi da Aminu Tambuwal, yayin da jam’iyyar ke ƙara jan hankalin manyan ‘yan siyasa.

Wannan sabon ci gaba na nuna yadda fafatawa ke ƙara tsananta a cikin haɗakar ‘yan adawa gabanin zaɓen 2027.

Da ɗumi-ɗumi: “Me ya sa har yanzu muke karɓo bashi a Najeriya?” —Sarki Sanusi ya tambayi dalilin cin ƙarin bashin gwamna...
24/04/2026

Da ɗumi-ɗumi: “Me ya sa har yanzu muke karɓo bashi a Najeriya?” —Sarki Sanusi ya tambayi dalilin cin ƙarin bashin gwamnati duk da cire tallafin man fetur.

Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, Sarkin kano Muhammadu Sanusi II, ya sake tayar da muhawara kan yadda bashin gwamnatin tarayya ke ci gaba da ƙaruwa duk da cire tallafin man fetur da aka ce zai rage nauyin kashe kuɗi.

Sanusi ya bayyana damuwa, inda ya tambayi dalilin da ya sa gwamnati ke ci gaba da karɓar sabbin basuss**a alhali an cire wani babban nauyi daga kasafin kuɗi ta hanyar janye tallafin mai.

Ya jaddada cewa cire tallafin ya k**ata ya ba gwamnati damar daidaita harkokin kuɗi, rage gibin kasafi, da kuma gujewa ƙarin bashi. Amma a cewarsa, akasin haka ne ke faruwa — bashin na ci gaba da hauhawa.

sarkin na Kano ya kuma bukaci a yi cikakken bayani ga ‘yan ƙasa kan yadda ake tafiyar da kuɗaɗen da aka samu bayan cire tallafin, domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana.

Address

Gwaram LGA
Old Gwaram

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nigeria News update posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Nigeria News update:

Share