04/06/2026
Martani Kan Maganar Prof. Abdullahi Bappah Garkuwa
‎
‎Abin mamaki ne yadda wasu s**a dauki kalaman Professor Garkuwa s**a karkatar da ma'anarsu saboda sabanin siyasa.
‎
‎Professor bai ce majalisar Sheikh Sharif Sale ita ce daidai da Majalisar Manzon ALLAH (SAW) a daraja ko matsayi ba. Abin da ya bayyana shi ne abin da ya gani na natsuwa, ladabi, tarbiyya, da girmama addini, wanda ya tuna masa da irin kyawawan siffofin da ake koyarwa a cikin Sunnah ta Manzon ALLAH (SAW).
‎
‎Ai a cikin Al-Qur'ani da Hadisi an umurce mu da koyi da Manzon ALLAH (SAW) a halaye, mu'amala, tausayi, kyauta, ladabi da tsoron ALLAH. Saboda haka idan aka ga mutum ko wata majalisa tana bayyana wasu daga cikin wadannan siffofi, a yaba mata da cewa tana bin tafarkin Manzon ALLAH (SAW), wannan ba laifi ba ne kuma ba sabon abu ba ne.
‎
‎Misali, idan aka ce wani yana koyi da Annabi (SAW) wajen kyauta, sadaka, gaskiya, sanya hula, tsaida gemu ko kyakkyawar mu'amala, babu mai hankali da zai fahimci cewa an daidaita shi da Annabi (SAW) a matsayi. Ana nufin ya yi koyi ne da wasu daga cikin halayensa masu kyau.
‎
‎Don haka, wadanda suke kokarin mayar da wannan magana laifi, ya kamata su fara kallon manufar magana kafin su yanke hukunci. Bambancin siyasa bai kamata ya sa a juya gaskiya ko a dora wa mutum abin da bai fada ba.
‎
‎Mu kasance masu adalci a yabonmu da kuma s**armu. Idan mutum ya fadi magana mai kyau, a karbe ta a matsayin alheri komai bambancin ra'ayi ko siyasa da ke tsakaninmu.
‎
‎ALLAH Ya shiryar da mu zuwa ga gaskiya, Ya sa mu zama masu adalci a magana da hukunci. Aameen 🤲.
‎
‎digital imam online
‎4rd June, 2026