14/09/2024
Yau Shekaru 7 Da Rasuwar Lil Ameer
A Rana Mai Kamar Ta Yau 14 Ga Watan Satumba 2017 ALLAH Yayiwa Mawakin Hausan Nan Ameer Isah Hassan Wanda Aka Fi Sani Da (LIL AMEER) Rasuwa,
Anayi Masa Lakabi Da AUTAN MAWAKA An Haifi Lil Ameer A Ranar 22 Ga Watan June 2003 Ya Rasu Yana Da Shekaru 14 A Duniya.
Ameer Isa Hassan (wanda a ka fi sani da Lil Ameer) ya rasu ranar 14 ga watan Satumba, 2017, a garin Kano sanadiyar hatsarin mota.
Haifafan dan jihar Kano, an haifi Marigayi Lil Ameer a cikin 2003 a birnin Kano. Har zuwa lokacin rasuwarsa, mawakin ya na koyan darasi a makaranta, duk da kasancewar shi wanda ya fara shahara a harkar wakoki marigayi bai bari harkar ta dauki hankalinshi wajen koyan darasi ba.
Ya kan tafi makarantar boko kuma idan ya tashi ya je ta islamiyya. Sai karshen mako ya ke samun damar yin aikin waka. Ameer ya canza makarantu da dama domin masoyansa su kan takura masa idan ya na koyon darasi. Babban burin marigayi shi ne in ya gama karatu ya zama matukin jirgin sama (Pilot).
Hakika iyayensa ne su ka ba shi damar fara waka kuma mahaifiyarsa ta ke taimaka ma sa wajen rubuta wakokin, domin ya fara waka tun ya na aji daya a karamar sakandare (JJS 1).
Matashin ya tashi ne da muradin waka tun ya na dan kankani. Ya fara waka ne domin ya nuna wa duniya cewa matasa daga yankin arewacin kasar nan na iya rera waka kuma su yi nasara.
Ya samu damar yin wakoki da dama kuma ya yi wasa tare da sauran shaharrun mawaka k**ar su Classik, Dj Abba, BOC da dai sauransu. Daga cikin garuruwan da marigayi ya samu damar halarta wasa akwai Kaduna, Kano da dai sauransu.
Cikin wakokin da marigayi ya yi akwai “Boss”, “Champion”, “Ilimin Boko Da Addinin Musulunci”, “Dance For Me”, “Baby Hello”, Hakan Ta Ke”, “Lifehood”, “Alhamdulillah”, “So Fly” da dai sauransu.
Tabbas abu ne mai wahala a sake samun karamin yaro k**ar Lil Ameer, wanda ya yi shuhura haka bisa la’akari da karancin shekarunsa. A lokacin da a ke tsaka da ta’aziyyar marigayin, Farfesa Abdalla Uba Adamu ya taba sha