27/07/2024
Gamayyar Ƙungiyoyi Sama Da Talatin Da Ke Shirin Fita Zanga-Zanga A Jihar Kogi Sun Janye
Mu kungiyoyin fararen hula a karkashin kungiyar Concerned Civil Society Organisations a jihar Kogi muna son yin kira ga ‘yan Najeriya musamman matasan jihar Kogi da kada su shiga cikin kiran da ake yi na zanga-zangar kasa a Najeriya. Mun ga hakan ya zama wajibi da kuma abin damuwa wajen ba ‘yan Najeriya da matasan Kogi musamman wajen musu nasihar kada su amsa kiran duk wata zanga-zanga a ko’ina a fadin jihar.
The Concerned Civil Society Organisation a jihar Kogi, hadaddiyar kungiyar matasa sama da talatin ne, kungiyoyin mata, masu sana’a da kungiyoyin farar hula, muna so mu bayyana cewa duk da yake hakkin kowane dan kasa ne ya yi zanga-zanga, dole ne kuma a yi la’akari da muhimman abinda ya dace. A kaucewa baragurbi wanda yakan kai ga halaka mutane da dukiyoyi kamar yadda aka shaida a karshen zanga-zangar ENDSARS.
Mun nemi sanin wadanda ke da hannu a wannan zanga-zangar, saboda fargabar da muke, har ya zuwa yau, ba a gano wani ko gungun jama’a da ke kiran wannan zanga-zangar ba, kuma wasu marasa kishi da fuska biyu za su iya jagorantar mu don mu yi zanga-zangar. Har ila yau, yana da mahimmanci mu yi la'akari da cewa dole ta wata fuskar ya kamata a zargi gwamnati mai ci gaba daya a wahalan da ake ciki a halin yanzu.
A yau ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cika shekara daya da wata daya da kwana ashirin da hudu a kan karagar mulki a matsayin shugaban kasa, don haka ya dace a ba shi lokaci domin ya juya al’amura. A bayyane yake kuma gaskiya ne cewa tattalin arzikin Najeriya yana cikin wani yanayi mara kyau kuma yana tafiya ta hanyar dawo da martaba, al'ummar kasar na shiga wani lokaci mafi tsanani a tarihi, amma zanga-zangar ba ita ce mafita ga matsalarmu nan take ba, sai dai mu cigaba da shiga cikin gwamnati tare da tattaunawa da gwamnatin ta hanyar da ta dace.
’Yan uwa Matasan Jihar Kogi, Najeriya ba za ta iya dakatar da ayyukanta na tattalin arziki gaba daya ba, saboda wadannan tsare-tsare da ake shirin yi domin kasar, ba za ta iya farfadowa daga illar da ake shirin yi ba, kasashe irin su Sudan, Libya da Yemen sun lalace gaba daya har zuwa yau sakamakon rikicin 'yan kasa suna tada tarzoma ga gwamnatocinsu. Najeriya ba za ta iya daukar irin wannan halin ba, dole ne mu ci gaba da yin kira ga talakawa ta yadda ba zai zama mun kara wa ƙasar wahalhalu da abin da take ciki ba.
Sai dai kuma muna son jawo hankalin Gwamnati da ta gaggauta magance wadannan abubuwa kamar haka:
1- Magance hauhawar farashin da ya tashi daga 22.8 a 2023 zuwa 34.2 a Yuni 2024.
2- Kawo ƙarshen rashin tsaro a Najeriya.
3- Tabbatar da isasshen abinci ga 'yan Najeriya ta hanyar kare gonakanmu.
4- Sake dawo da farashin kuɗin makaranta na ɗalibanmu da ke karatu a manyan makarantu.
5- Dawo da farashin wutar lantarki.
6- abunta matatun mai don samun ƙarfin aiki mai inganci.
7- Rage farashin gudanar da gwamnati a duk matakai. Idan aka yi la'akari da abubuwan da ke sama za su dawo da Najeriya kan hanyar ci gaba da wadata.
Gwamnonin jihohi a Najeriya suma dole ne su tashi ta hanyar zuba jari cikin aikin gona da tsaro musamman yadda aka gani a Jihar Kogi da Gwamna Ahmed Usman Ododo wanda ya nuna ƙoƙari don ɗaukar Jihar Kogi zuwa alkibla. Muna nanata cewa idan duk jihohi za su zuba jari cikin samarwa fiye da cinye, to tattalin arziki zai sake dawowa da ƙarfi.
Sa hannu
Abubakar Onimisi