Potiskum Media News

Potiskum Media News Potiskum Media News – Tushen Gaskiya, Madogarar Jama’a...

Burin mu shi ne mu zama amintaccen tushe na gaskiya ga jama’a, ba tare da shishigi ko son zuciya ba.

Allah Ya Ƙara Ɗaukaka

JIHAR YOBE: Alhamdullah mai girma gwamna Hon mai mala buni muna godiya da kokarinka na  tabbatar da jagoran matasa Dr Mo...
07/08/2026

JIHAR YOBE: Alhamdullah mai girma gwamna Hon mai mala buni muna godiya da kokarinka na tabbatar da jagoran matasa Dr Mohammed Goje yazama cikyakkyan SSG...

Matashin ya ƙara da cewa ‎In dai da goje a yobe kowa ya goge hawayen sa ‎Yau ranar farin cikin matasan jahar yobe ne

Potiskum Media News

DA ƊUMI ƊUMI: Gwamna Buni Ya Bayyana Dalilan Naɗin Dr. Mohammed Goje A Matsayin Cikakken SSGGwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai...
06/08/2026

DA ƊUMI ƊUMI: Gwamna Buni Ya Bayyana Dalilan Naɗin Dr. Mohammed Goje A Matsayin Cikakken SSG

Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, CON, COMN, ya bayyana cewa naɗin Dr. Mohammed Goje a matsayin cikakken Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG) ya samo asali ne daga ƙwarewarsa, jajircewarsa da irin yadda ya gudanar da aikinsa tun lokacin da aka naɗa shi a matsayin mukaddashin SSG.

A cewar Gwamnan, Dr. Goje ya nuna babban matakin jajircewa, aminci, saurin gudanar da aiki da kuma ƙwarewar shugabanci, lamarin da ya sa ya cancanci ci gaba da riƙe muƙamin.

Gwamna Buni ya kuma bayyana cewa gwamnatin sa na haɗa gogaggun ma'aikata da matasa masu ilimi da ƙwarewar fasahar zamani domin inganta ayyukan gwamnati da daidaita jihar da sauye-sauyen zamani.

Ya ƙara da cewa ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha muhimmin ginshiƙi ne na daidaita ayyukan gwamnati, tare da tabbatar da haɗin gwiwa tsakanin ma'aikatu, hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki domin inganta ayyukan gwamnati da hidimtawa al'umma.

Potiskum Media News

INNALILLAHI: Allah yayi wa Alhaji Jibir Janko Rasuwa ɗaya daga cikin dattawan garin Potiskum...Har zuwa yanzu ba'a sanar...
05/08/2026

INNALILLAHI: Allah yayi wa Alhaji Jibir Janko Rasuwa ɗaya daga cikin dattawan garin Potiskum...

Har zuwa yanzu ba'a sanar da lokacin jana'izar ba...

Allah ya jikansa da rahama...

DA ƊUMI ƊUMI: Gwamna Buni Ya Naɗa Dr. Mohammed Goje A Matsayin Cikakken Sakataren Gwamnatin Jihar YobeGwamnan Jihar Yobe...
05/08/2026

DA ƊUMI ƊUMI: Gwamna Buni Ya Naɗa Dr. Mohammed Goje A Matsayin Cikakken Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe

Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, CON, COMN, ya amince da naɗa Dr. Mohammed Goje a matsayin cikakken Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe (SSG).

Dr. Goje ya fara riƙe muƙamin ne a matsayin Mukaddashin SSG tun ranar 29 ga Afrilu, 2026, bayan ya yi aiki a matsayin Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA).

Yayin da yake taya shi murna, Gwamna Buni ya buƙaci Dr. Goje da ya tabbatar da amincewar da aka yi da shi ta hanyar ƙara inganta shugabanci nagari da ingantaccen gudanar da ayyukan gwamnati domin ci gaban Jihar Yobe.

Potiskum Media News

GARIN POTISKUM: Hon. Ishaku Guza  ne dan siyasar da ya cancanci cigaba da wakiltar al'ummar potiskum central 2027...Miye...
05/08/2026

GARIN POTISKUM: Hon. Ishaku Guza ne dan siyasar da ya cancanci cigaba da wakiltar al'ummar potiskum central 2027...

Miye zaku ce?

DA ƊUMI ƊUMI: Shirin Renewed Hope Ya Tallafa Wa Mutane 50 Masu Nakasa A PotiskumShirin Renewed Hope ya tallafa wa mutane...
04/08/2026

DA ƊUMI ƊUMI: Shirin Renewed Hope Ya Tallafa Wa Mutane 50 Masu Nakasa A Potiskum

Shirin Renewed Hope ya tallafa wa mutane 50 masu nakasa a Ƙaramar Hukumar Potiskum, Jihar Yobe, ta hanyar ba su tallafin kuɗi domin inganta rayuwarsu da ƙarfafa dogaro da kai.

An yaba wa Hon. Mohammed Abba Isa, Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Mutane Masu Buƙata ta Musamman, kuma National Director na Persons with Disabilities Affairs a City Boy Movement, bisa jagorancinsa da goyon bayan da ya bayar wajen aiwatar da shirin.

Haka kuma, an jinjinawa Haruna Tata Buduwa, Mai Gudanarwa na City Boy Movement a Jihar Yobe kan Harkokin Mutane Masu Nakasa, saboda jajircewarsa da kyakkyawan tsari da s**a tabbatar da nasarar shirin.

Masu shirya shirin sun jaddada aniyarsu ta ci gaba da samar da damammaki da tallafa wa mutane masu buƙata ta musamman domin gina al'umma mai haɗin kai da ci gaba.

Potiskum Media News

GARIN POTISKUM: Matashi Ɗan Potiskum Ya Samu Tallafin Karatu Na Kusan Naira Miliyan 45 A Jami'ar AUNWani matashi ɗan asa...
04/08/2026

GARIN POTISKUM: Matashi Ɗan Potiskum Ya Samu Tallafin Karatu Na Kusan Naira Miliyan 45 A Jami'ar AUN

Wani matashi ɗan asalin garin Potiskum a Jihar Yobe, Gaddafi Muhammad Ismail, na ci gaba da ɗaga tutar garinsa bayan samun cikakken tallafin karatu daga World Assembly of Muslim Youth (WAMY) ta ƙasar Saudiyya.

Gaddafi na karatun Faculty of Law a American University of Nigeria (AUN), Yola, inda aka kiyasta darajar tallafin karatunsa ta kai kusan Naira miliyan 45.

A cewarsa, shi ne kaɗai ɗan asalin Potiskum da ke cin gajiyar wannan shirin na tallafin karatu a jami'ar.

Ya bayyana cewa burinsa shi ne ya kammala karatunsa cikin nasara, ya zama ƙwararren lauya mai kishin gaskiya da adalci, tare da amfani da iliminsa wajen yi wa al'umma da ƙasa hidima.

Potiskum Media News

ABUN A YABA: Ina mai  bawa Yaran Gidana Haƙuri Koda Siyasa Ko Babu Siyasa Muna Tare Kuma In Sha Allahu Zan Taimaki Duk W...
04/08/2026

ABUN A YABA: Ina mai bawa Yaran Gidana Haƙuri Koda Siyasa Ko Babu Siyasa Muna Tare Kuma In Sha Allahu Zan Taimaki Duk Wanda Yamun Wahala A Siyasa A Matsayina Na Dan Kasuwa.

Sakon Hon Usman Ali Suleiman zuwa ga yaran gidan sa.

Potiskum Media News

MASHA ALLAH: Mai Martaba Sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi tare da Abokin karatunsa "Course Mates" yayin yin lecture....P...
04/08/2026

MASHA ALLAH: Mai Martaba Sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi tare da Abokin karatunsa "Course Mates" yayin yin lecture....

Potiskum Media News

GARIN POTISKUM: Wannan shine matashi Abbakar zakari Yarima Gwarzon shekara na gasar Alkur'ani mai girma na garin Potisku...
03/08/2026

GARIN POTISKUM: Wannan shine matashi Abbakar zakari Yarima Gwarzon shekara na gasar Alkur'ani mai girma na garin Potiskum...

Wanne Fata Kuke masa?

Potiskum Media News

Address

Potiskum

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Potiskum Media News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Potiskum Media News:

Shortcuts

Share