Yobe Voice Tv

Yobe Voice Tv Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Yobe Voice Tv, TV Channel, Yobe State, Potiskum local Government, Potiskum.

An K**a Makahoʻ Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi A Garin Gwoza
18/06/2026

An K**a Makahoʻ Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi A Garin Gwoza

DA DUMI-DUMI: Sabbin Gidajen Alƙalai Zasu Ƙarfafa Dimokuraɗiyyar Najeriya — Inji TinubuShugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu,...
18/06/2026

DA DUMI-DUMI: Sabbin Gidajen Alƙalai Zasu Ƙarfafa Dimokuraɗiyyar Najeriya — Inji Tinubu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gina sabbin gidajen zama na alƙalai zai taimaka wajen ƙarfafa tubalin dimokuraɗiyyar Najeriya.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan muhimmancin jin daɗin ma’aikatan shari’a domin tabbatar da adalci da ingantaccen tsarin shari’a a ƙasar.

Ya ce gwamnati na ci gaba da ɗaukar matakai da nufin inganta aikin shari’a da kuma tallafawa cibiyoyin dimokuraɗiyya.

Mezakuce?

Sarakunan Arewa Na Gudanar Da Taro A Jihar JigawaTaron dai na zuwa ne a daidai lokacin da yankunan Arewa ke fama da mats...
16/06/2026

Sarakunan Arewa Na Gudanar Da Taro A Jihar Jigawa

Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da yankunan Arewa ke fama da matsalolin tsaro.

Me za ku ce?

Za'a katse sabis na tsawon watanni 5 a wasu ƙananan hukumomin jihohin Najeriya da s**a haɗa da Zamfara Katsina Kebbi Sok...
15/06/2026

Za'a katse sabis na tsawon watanni 5 a wasu ƙananan hukumomin jihohin Najeriya da s**a haɗa da Zamfara Katsina Kebbi Sokkoto Kaduna Niger da Kano don magance matsalar tsaro—NCC. K**ar yadda jaridar Nigeria daily times ta wallafa.

Me zaku ce?

DA ƊUMI ƊUMI: Mukaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe, Dr. Mohammed Goje, ya miƙa takardar naɗi ga sabon Sarkin Ngaza...
15/06/2026

DA ƊUMI ƊUMI: Mukaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe, Dr. Mohammed Goje, ya miƙa takardar naɗi ga sabon Sarkin Ngazargamu, Alhaji Yerima Ibn Mahmud, bayan amincewar Gwamna Mai Mala Buni da naɗinsa.

Naɗin ya biyo bayan rasuwar marigayi Sarkin Ngazargamu, Alhaji Ahmad Tijjani Ibn Saleh Geidam. Kafin hawansa karagar mulki, Alhaji Yerima Ibn Mahmud ya kasance Turakin Ngazargamu, inda ya yi hidima a muƙamai daban-daban na gwamnatin jihar Yobe.

An yi addu’ar Allah Ya ba sabon sarkin hikima, adalci da jagoranci nagari domin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Masarautar Ngazargamu.

Yobe Voice TV

TIRƘASHI: Zamu fara tafiya da manyan 'yan social media zuwa filin Yaƙi da ta’addanci domin su sheda irin ƙoƙarin da sojo...
15/06/2026

TIRƘASHI: Zamu fara tafiya da manyan 'yan social media zuwa filin Yaƙi da ta’addanci domin su sheda irin ƙoƙarin da sojojin ke yi wurin Yaƙi da 'yan bindiga...

Yi Mana Tagging Ɗin Ɗan Social Media guda ɗaya da kake so a tura shi Yaƙi...

SUBHANALLAH: Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram/ISWAP ne sun ƙone makarantar firamare da sakandare da ke ƙauyen Kauti...
15/06/2026

SUBHANALLAH: Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram/ISWAP ne sun ƙone makarantar firamare da sakandare da ke ƙauyen Kautikari a ƙaramar hukumar Chibok ta jihar Borno.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fargaba kan ɗaliban M***a Primary and Junior Secondary School da ke Askira-Uba, waɗanda aka sace kusan wata guda da ya gabata ba tare da samun labarinsu ba.

Miye Zaku ce?

DA ƊUMI ƊUMI: Hazikin matashi kuma shugaban ƙungiyar Damuli Youths Movement for BMW Yobe South, Musa Bello, ya sake ɗauk...
15/06/2026

DA ƊUMI ƊUMI: Hazikin matashi kuma shugaban ƙungiyar Damuli Youths Movement for BMW Yobe South, Musa Bello, ya sake ɗaukar wani mataki na tallafa wa al’umma ta hanyar ɗaukar nauyin horas da mata 100 kan yadda ake haɗa sabulu da liquid soap.

An gudanar da shirin ne ƙarƙashin jagorancin MD Damuli Investment, Commander Alhaji Liman Machina Dabuwa, domin ƙarfafa mata da samar musu da dabarun dogaro da kai.

Mahalarta taron sun yabawa wannan ƙoƙari, suna mai bayyana shi a matsayin wani muhimmin mataki na bunƙasa sana’o’i da tallafa wa mata a yankin.

Yobe Voice TV

DA ƊUMI ƊUMI: Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya kafa kwamitin bincike domin nazarin albashi da walwalar ma’aikatan k...
11/06/2026

DA ƊUMI ƊUMI: Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya kafa kwamitin bincike domin nazarin albashi da walwalar ma’aikatan koyarwa na Yobe State University.

Sanarwar da Mukaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar, Dr. Mohammed Goje, ya fitar ta ce kwamitin zai ziyarci wasu jami’o’in jihohi a Najeriya domin nazarin tsarin albashi, alawus-alawus da hanyoyin inganta walwalar ma’aikatan jami’a.

Kwamitin wanda Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi na jihar, Farfesa Muhammad Bello Kawuwa, ke jagoranta, zai kuma duba hanyoyin samar da kuɗaɗe da kyawawan dabarun gudanar da jami’o’i domin taimaka wa gwamnatin jihar wajen yanke shawarar da za ta inganta fannin ilimi mai zurfi.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa matakin na daga cikin ƙoƙarinta na ƙarfafa ilimi da inganta jin daɗin ma’aikatan jami’o’i a jihar Yobe.

NANGERE: Ba jam'iyya ko kuɗi za mu duba ba, za mu duba cancanta, nagarta da wanda zai yi wa al'umma hidima.Cewar Dattijo...
11/06/2026

NANGERE: Ba jam'iyya ko kuɗi za mu duba ba, za mu duba cancanta, nagarta da wanda zai yi wa al'umma hidima.

Cewar Dattijon Ɗan Siyasa Alhaji Barde Hamma

Wanne fata kuke masa?

Address

Yobe State, Potiskum Local Government
Potiskum

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Yobe Voice Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share