14/09/2025
SUNAYEN KOFOFIN AL-JANNAH GUDA TAKWAS (8).
Al-jannah mazauni ne da Allah Madaukakin sarki ya tanadar ma nayinsa wadanda S**a yi mashi da'a wajen bauta mashi ta hanyar shaidawa babu abin bautawa da gaskiya Sai ALLAH Kuma Annabi Muhammad Manzonsa ne, Kuma S**a kiyaye hukunce-hukuncen addinin musulunci sannan S**a mutu suna musulmai.
Kamar yadda aka ruwaito daga Ubaadah (RA) Manzon Allah (SAW) ya ce:
"Duk wanda ya shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, ba shi da abokin tarayya, kuma Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, kuma Annabi Isa bawan Allah ne kuma ManzonSa ne, kuma kalmar da Allah Ya yi wa Maryama da ManzonSa ne. ruhin da Ya halitta (cf. al-Nisa' 4:171), kuma Aljanna gaskiya ce, kuma Jahannama gaskiya ce, Allah zai shigar da shi Aljanna ta kowace kofa takwas da ya so, domin na kyawawan ayyukansa.” (Bukhari 3180).
Sunayen wasu daga cikin kofofin Jannah a Musulunci sune:
1- Baab Al-hajji: Wannan kofa ta wadanda s**a kammala aikin Hajji ne, aikin hajjin Makka.
2-Baabus Salaah: Wannan kofa tana ga wadanda s**a kasance masu tsayuwar sallah.
3- Jihad Baabul: Wannan kofa ta wadanda s**a yi jihadi ne.
4-Baabus Sadaqah: Wannan kofa ta kasance ga masu yawaita yin Sadaqah.
5- Baabur Rayyaan: Wannan kofa ta masu yin azumi ne.
6- Baabul Kaazimeenal Ghaiz Wal 'Aafina 'Anin Naas: Wannan kofa ta masu danne fushi ne, kuma suke yafewa wasu.
7- Baabul Aiman: Wannan kofa ta wadanda s**a tsira daga hisabi da azaba.
8-Baabuz Zikiri: Wannan kofa ta masu yawan ambaton Allah ne.
ALLAH MADAUKAKIN SARKI, YA NI'IM TAMU DA AL-JANNARSA DAN RAHAMARSA.
Mallam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum