28/06/2025
Musa Musa Yakubu
(El-Yakub Shuraim)
GIDAUNIYAR "CHARITABLE FOUNDATION" TA GUDANAR DA GASAR KACI-CI-KACI-CI NA GORON SALLAR WANNAN SHEKARAR
Kamar yadda gidauniyar ta saba gabatarwa a kowace shekara yayin bukukuwan sallar Layya, wannan karon ma ta gabatar da gasar a babban ɗakin taron "Multi purpose" dake Kwalejin ilmi, fasaha da koyon ƙere-ƙere na tarayya dake ƙaramar hukumar Pataskamu.
Koda yake, gidauniyar da cibiyar tata ke ƙaramar hukumar ta Pataskamu a jihar Yobe, ta faro shirye-shiryen nata na baya ne da gudanar da gasar karatun Alƙur'ani mai girma, sai dai a wannan karon ta sauya tsarin shirye-shiryen nata ne zuwa gabatar da gasar kaci-ci-kaci-ci wajen sanin ilmummukan dake taimakawa akan sanin ma'anonin Alƙur'ani.
Kafar watsa labarai ta AABC Hausa ta ruwaito cewa: "A wata amsar tambayar daya bayar, shugaban gidauniyar Ustadz Suhailu Musa Ɗahiru yace: "Manufar kafa gidauniyar itace dawo da hankulan ɗalibai mahaddata Alƙur'ani daga ɗebe hankulansu da wasu shirye-shirye na raye-raye, kaɗe-kaɗe da guje-guje da ake gudanarwa a lokutan bukukuwan sallolin Azumi da Layya s**a yi".
Shugaban yace: "Mafi akasari zaka ga ƙarfin haddar ɗalibai yana samun rauni a dalilin halartar wasu taruka da ake gabatarwa a bukukuwan salla wanda suna halarta ne a rashin wasu taruka masu amfanarwa da s**a shafi harkokin addini", inda yaci gaba da cewa, "ganin haka ne yasa muma muka ɓullo da wannan shirin. Domin idan akwai shirin daya shafi addini, to su ɗaliban ba zasu halarci waɗancan tarukan shirmen dake kawo musu koma bayan karatun Alƙur'aninsu ba".
Koda na tambayeshi ta kafar manhajar WhatsApp kan dalilin da yasa gidauniyar tayi turjiya ga barin gudanar da gasar akan abin daya shafi haddar Al'ƙur'ani mai girma, sai shugaba Ɗahirun yace: "To dalili shine, lalle mun ɗauki tsawon shekaru uku muna gabatarwa akan haddar Alƙur'ani mai girma, to amma kasan yau da gobe idan kana aiwatar da wani shiri, zaka riƙa cin karo da sabbin ci gaba da kuma wasu matsaloli da ka iya ɓullowa tare da samun hanyoyin magancesu. Don haka, mun lura da cewa galibi makarantu da duk wasu cibiyoyi da suke gabatar da gasa s**an gabatar ne akan haddar Alƙur'ani. Sannan alhamdulillahi, a nazarinmu mun gano cewa a yanzu an samu abinda ake buƙata na yawan mahaddata Alƙur'ani a garin Pataskamu. A dalilin haka muka ga ya kamata mu faɗaɗa manufar tafiyar zuwa ga ilmantar da yara sanin ilmin ma'anonin Alƙur'ani mai girma, tunda bayan hadda ɗin yana da kyau ɗalibi ya san cewa akwai wani sabon abu kuma daya kamata ya sani dangane da Alƙur'ani ba wai ya ɗauka cewa don ya kai matakin kammala haddar Alƙur'ani kuma shike nan ba".
Shirin Taskar labarai na gidan rediyon tarayya Sunshine FM na garin Pataskamu ya ruwaito cewa: "Taron ya samu halartar makarantu 11 daga cikin 15 da aka gayyata, inda ƴan takara 31 s**a samu damar fafatawa".
Har ila yau, kafar labaran AABC, a bayanin data wallafa a shafinta na Facebook tace: "Shugaban gidauniyar, Ustadz Suhailu Musa Ɗahiru ya bayyana cewa: "Tun kafa gidauniyar mun gabatar da gasar haddar Alƙur'ani mai girma har karo uku a jere a kowace shekara, inda a karo na farko muka gabatar da gasar bayan kammala "Daura" a masallacin Juma'ar da ake kira masallacin Waziri, inda muka samu ƴan takara daga matakin izu 3 zuwa na izu 40. A shekarar data kewayo kuma wacce itace karo na biyu, mun gabatar ne a babban ɗakin taron dake sakatariyar ƙaramar hukumar Pataskamu, shima mun samu ƴan takarkaru daga matakin izu 3 har zuwa na 40. Sai kuma karo na ƙarshe wanda daga shine muka sauya tafiyar daga tsarin gasar haddar Alƙur'ani zuwa tsarin gasar kaci-ci-kaci-cin sanin ilmin ma'anonin Alƙur'ani. Shi kuma mun gabatar da shine a ɗakin taro na IBB dake kwalejin tarayya na garin Pataskamu, inda muka samu ƴan takarkaru daga izu 3 har zuwa izu 60 kuma haƙiƙa muna yiwa Allah godiya bisa wannan ni'imar domin Alhamdulillahi muna samun nasara".
A tsarin gudanar da gasar, gidauniyar kan gabatar da gayyata ne ga makarantun dake garin na Pataskamu bisa buƙatar ƴan takarkaru 2 a kowane izu da gidauniyar ta buƙata gwargwadon girma ko ci gaban makaranta.
Haka kuma, gidauniyar ta tsara gasar kaci-ci-kaci-cin ne bisa tsarin rukuni-rukuni. Rukunin A, rukunin B da kuma rukunin C tare da shirya tambayoyi 60 inda ta raba tambayoyin 60 zuwa gida 3, ya kasance tambayoyi ashirin-ashirin ga kowane rukuni, sannan ta gabatar da tambayoyi 20 izuwa ga kowane rukuni daga rukunnan na A, B da kuma C inda kowane ɗan takara zai amsa tambayoyi daga jerin tambayoyin da aka gabatarwa rukuninsa.
A sakamakon gasar, ƴan takara 2 ne s**a yi ragas s**a zamto gwarazan shekara. Waɗannan ɗalibai sune Asiya Usman Ibrahim daga makarantar Al-Minnah International Academy dake unguwar "Tandari" wacce kuma ta fito daga rukunin "A". Ɗalibar ta samu nasarar zuwa na ɗaya ne da jimillar maki 400 inda ta samu makin na abareji 100. Sai kuma ɗaya ƴar takarar Maryam Abdullahi Adamu da tazo daga makarantar Mu'assasah Adamu Idi dake unguwar "Central" wacce ita ma ta fito daga rukunin na "A" ta kuma kasance na 1 da maki 400 inda ita ma ta samu jimillar maki 100 bisa tsarin abareji.
Gasar ta samu halartar ƴan takarkaru 31 da s**a fafata inda ɗalibai 2 su kayi kunnen doki a lamba na 1, sai lamba na 2 da aka samu ɗalibi 1, kana lamba na 3 kuma aka samu ɗalibai 3 dasu kayi kunnen doki. Haka kuma lamba na 4 ƴan takara 3 ne su kayi ragas a yayin da aka samu ɗalibi 1 da yazo na biyar shi kaɗai a lamba na 5.
Wannan gasar ta gudana ne ƙarƙashin alƙalancin Mallam Shaikh Rabi'u Alhaji Abdullahi; shugaban alƙalai, Mallam Ibrahim Haruna Musa; sakatare, Ustadz Abubakar Z***r Yarima, Ustadz Anas Abdullahi Maikuɗi, Mallam Alhassan Saleh; mai lura da lokaci.
A bayanin da AABC ta fitar, "Gidauniyar an assasata ne a 1st, Agusta, 2022 kuma daga wannan lokacin ta riƙa gudanar da muhadarori a duk hutattakin da gwamnati ta riƙa bayarwa na makarantu. Gidauniyar tace ta gabatar da muhadarori akan ilmin Tajwidi musamman kan abin daya shafi "Tafkhimi da kuma Al-Ghunna".