YOBE News FORUM

YOBE News FORUM Barka da zuwa YOBE News FORUM
Amintacciyar majiyar labarai, nazari da rahotanni masu inganci daga Yobe, Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

Muna aiki da gaskiya, daidaito da amincewa. Ku biyo mu domin samun labarai a kan lokaci.

DA ƊUMI ƊUMI: Gwamna Buni Ya Samu Lambar Yabo Ta Ƙasa da Ƙasa Kan Kyakkyawan MulkiAn karrama Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji ...
03/07/2026

DA ƊUMI ƊUMI: Gwamna Buni Ya Samu Lambar Yabo Ta Ƙasa da Ƙasa Kan Kyakkyawan Mulki

An karrama Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, da lambar yabo ta ƙasa da ƙasa bisa kyakkyawan shugabanci da ayyukan ci gaban al'umma da gwamnatinsa ke aiwatarwa.

An ba shi lambar yabon ne a birnin Landan, karkashin shirin African Business Leadership Awards (ABLA), inda aka yabawa nasarorin da gwamnatin Yobe ta samu a fannonin lafiya, ilimi da noma.

Gwamna Buni ya sadaukar da wannan nasara ga al'ummar Jihar Yobe, yana mai cewa hakan zai ƙara masa ƙwarin gwiwar ci gaba da yi wa jama'a aiki da gaskiya da rikon amana.

Mai Rahoto
Dalha Idi Tela

Yau 05/06/2026 Ake Bikin Bada Rank Na Copral a Yindiski Division Potiskum Mai RahotoDalha Idi Tela
05/06/2026

Yau 05/06/2026 Ake Bikin Bada Rank Na Copral a Yindiski Division Potiskum

Mai Rahoto
Dalha Idi Tela

🔴 'YAN SANDAN YOBE SUN BANKADO WURIN KERA BINDIGOGI BA BISA KA'IDA BA A POTISKUM, SUN K**A MUTANE BAKWAIRundunar 'Yan Sa...
04/06/2026

🔴 'YAN SANDAN YOBE SUN BANKADO WURIN KERA BINDIGOGI BA BISA KA'IDA BA A POTISKUM, SUN K**A MUTANE BAKWAI

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Yobe ta samu wani gagarumin nasara a kokarinta na yaki da aikata laifuka bayan da ta bankado wata maboyar kera bindigogi ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Potiskum.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar, ya bayyana cewa jami'an rundunar da ke karkashin Hedikwatar Yankin Potiskum tare da hadin gwiwar jami'an ofishin 'yan sanda na yankin sun gudanar da wani samame bisa sahihan bayanan sirri.

An kai samamen ne zuwa wani wajen aikin maƙera da ke Tasha Adua a kan titin Danchuwa da ke Potiskum, inda aka k**a mutane bakwai da ake zargi.

Kayan da aka samu a wurin sun hada da bindigogi biyu da aka kera a gida, bututun bindiga guda ashirin da hudu, kundukan bindiga guda tara, tsoffin bindigogin Dane guda hudu da ba sa aiki, na'urar goga karfe guda daya da kuma adda mai kaifi guda daya.

Rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran wadanda ke da hannu a lamarin, masu sayen mak**an da kuma manufar da ake son amfani da su.

Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Yobe, CP Usman Kanfani Jibrin, ya umarci jami'an da ke binciken lamarin da su kara kaimi wajen gano sauran wuraren kera mak**ai ba bisa ka'ida ba tare da tantance barazanar tsaro da irin wadannan ayyuka ke haifarwa.

Rundunar ta kuma gargadi al'umma da su guji bari a yi amfani da gidajensu ko wurarensu wajen gudanar da haramtattun ayyuka, musamman kera mak**ai masu hadari.

Haka kuma ta bukaci mazauna jihar da su kasance masu lura tare da gaggauta kai rahoton duk wani motsi ko aiki da ke haifar da zargi ga ofishin 'yan sanda mafi kusa ko sauran hukumomin tsaro.

Majiyar Labari: Rundunar 'Yan Sandan Jihar Yobe.

🔴 MU AJE SIYASAR JAM’IYYA, MU ZAƁI MUTANEN KIRKI — IBRAHEEM FARA FARAWani matashi mai rajin ci gaban al’umma, Ibraheem F...
24/05/2026

🔴 MU AJE SIYASAR JAM’IYYA, MU ZAƁI MUTANEN KIRKI — IBRAHEEM FARA FARA

Wani matashi mai rajin ci gaban al’umma, Ibraheem Fara Fara, ya buƙaci al’umma da su daina fifita siyasar jam’iyya wajen zaɓe, tare da mayar da hankali wajen zaɓar mutanen kirki masu gaskiya da kishin jama’a.

Ibraheem ya bayyana cewa ci gaban al’umma ba ya ta’allaka ga jam’iyya kaɗai, sai dai akan irin nagarta, amana, da ƙwarewar waɗanda ake zaɓa domin jagoranci.

A cewarsa: “Mu aje siyasa irin ta jam’iyya, mu zaɓi mutanen kirki a kowace jam’iyya s**a tsaya neman takara.”

Ya ƙara da cewa Najeriya na buƙatar shugabanni masu tausayi, gaskiya, da kishin jama’a domin samar da ingantaccen shugabanci da ci gaba mai ɗorewa.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin siyasa da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ci gaba da ɗaukar hankalin jama’a a faɗin ƙasar nan.

🔴 DR. IDRISS ADAMU IDI (DANCHUWA) YA JANYE DAGA TAKARAR MAJALISAR WAKILAI TA NANGERE/POTISKUMYobe News ForumDr. Idriss A...
17/05/2026

🔴 DR. IDRISS ADAMU IDI (DANCHUWA) YA JANYE DAGA TAKARAR MAJALISAR WAKILAI TA NANGERE/POTISKUM

Yobe News Forum

Dr. Idriss Adamu Idi (Danchuwa) ya sanar da janye takararsa daga neman kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Nangere/Potiskum Federal Constituency karkashin jam’iyyar APC.

A cikin wata sanarwa mai tsawo da ya fitar, Danchuwa ya bayyana matakin a matsayin wanda aka dauka domin kare hadin kai, zaman lafiya da muradun al’umma da jam’iyya sama da bukatar kai.

Ya gode wa al’ummar Nangere/Potiskum, magoya baya, matasa, dattawa, mata da shugabannin APC bisa irin goyon baya, addu’o’i da kaunar da s**a nuna masa tun bayan bayyana aniyarsa ta tsayawa takara.

Danchuwa ya ce bayan doguwar tuntuba da nazari kan halin siyasar da ake ciki, ya yanke shawarar janye takararsa cikin girmamawa ga shugabanci, hadin kai da kuma makomar jam’iyyar APC a jihar.

Ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan wasu muhimman abubuwa guda uku da s**a hada da kafa wani kwamiti na musamman da Gwamna Mai Mala Buni ya yi karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe, Dr. Mohammed Goje, domin tattaunawa da masu neman takara.

Haka kuma ya ce shugabanni da masu ruwa da tsaki daga Nangere/Potiskum sun roke shi da ya mutunta shawarar gwamnati tare da fifita hadin kai da zaman lafiya sama da buri na siyasa.

Danchuwa ya kara da cewa bayan tattaunawa da dattawa, iyaye da shugabannin da yake mutuntawa, ya ga dacewar ajiye bukatar kai domin moriyar jama’a baki daya.

Sai dai ya tabbatar wa magoya bayansa cewa wannan ba karshen tafiyar hidima ba ne, yana mai cewa zai ci gaba da taimakon al’umma da bayar da gudunmawa wajen cigaban mazaba, jihar Yobe da Najeriya baki daya duk lokacin da dama ta samu.

Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su kasance masu hakuri, biyayya ga doka da kuma ci gaba da mara wa jam’iyyar APC baya domin dorewar hadin kai da cigaban jihar Yobe.

Allah Ya albarkaci Nangere/Potiskum, Jihar Yobe da Najeriya baki daya.

🔴 HON. YAHAYA GARBA BELLO YA JANYE DAGA TAKARAR MAJALISAR TARAYYA TA NANGERE/POTISKUMYobe News ForumMai neman takarar ku...
17/05/2026

🔴 HON. YAHAYA GARBA BELLO YA JANYE DAGA TAKARAR MAJALISAR TARAYYA TA NANGERE/POTISKUM

Yobe News Forum

Mai neman takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar mazabar Nangere/Potiskum, Hon. Yahaya Garba Bello, ya sanar da janye takararsa bayan tuntuba da shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Jihar Yobe.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Hon. Yahaya Garba Bello ya bayyana godiyarsa ga Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, tare da shugabannin APC, dattawa da masu ruwa da tsaki bisa irin jagoranci, shawarwari da kokarin da suke yi domin tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a jam’iyyar da jihar baki daya.

Ya kuma gode wa magoya bayansa, abokai, ‘yan uwa da masu fatan alheri bisa addu’o’i, goyon baya da jajircewar da s**a nuna masa tun farkon wannan tafiya ta siyasa.

Hon. Yahaya Garba Bello ya ce bayan doguwar tuntuba da la’akari da maslahar jam’iyya, hadin kai da ci gaban al’umma sama da bukatar kai, ya yanke shawarar janye takararsa duk da cewa hakan bai kasance abu mai sauki ba.

Ya bayyana cewa tun daga farko manufarsa ba ta kasance son rai ko neman anfani na kai ba, illa yi wa al’umma hidima, kawo ci gaba da samar da kyakkyawan wakilci ga mutanen Nangere/Potiskum.

Sai dai ya tabbatar wa jama’a cewa ayyukan taimakon al’umma, tallafa wa mabukata, karfafa matasa da ci gaban al’umma da aka sanshi da su ba za su tsaya ba ko da babu mukami.

A karshe, ya yi kira ga magoya bayansa da su kasance masu hakuri, hadin kai da kuma ci gaba da bai wa zaman lafiya da ci gaban jihar muhimmanci.

Allah Ya albarkaci Nangere/Potiskum, Jihar Yobe da Najeriya baki daya.

🔴 GAGARUMIN NASARA A YOBE: FURSUNONI 25 SUN ZAUNA JARRABAWAR WAEC DA NECOYobe News ForumHukumar Gyaran Hali ta Najeriya ...
15/05/2026

🔴 GAGARUMIN NASARA A YOBE: FURSUNONI 25 SUN ZAUNA JARRABAWAR WAEC DA NECO

Yobe News Forum

Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya reshen Jihar Yobe ta bayyana wani gagarumin ci gaba a kokarinta na gyara hali, ilimantarwa da sake mayar da fursunoni cikin al’umma ta hanyar ilimi.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, DSC Abdullahi Adamu ya fitar, ya bayyana cewa fursunoni 25 daga gidan gyaran hali na Medium Security Custodial Centre da ke Potiskum sun samu damar zama jarabawar WAEC da NECO bayan shiri da horaswa ta musamman.

Sanarwar ta ce wannan nasara ta biyo bayan wata ziyara da Controller of Corrections na jihar, Ortsergah J. Terver, ya kai wa Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare, inda s**a tattauna hanyoyin kara bunkasa ilimi ga fursunoni a cibiyoyin gyaran hali na jihar.

Hukumar ta bayyana cewa binciken da aka gudanar ya nuna yawancin fursunonin matasa ne da ba su samu ilimi ba ko kuma s**a bar makaranta tun da wuri, lamarin da ya sa aka kafa cibiyar karatu a gidan gyaran hali na Potiskum domin ba su damar ci gaba da karatu.

Kwamishinan Ilimi ya yabawa wannan shiri, yana mai bayyana shi a matsayin wani muhimmin mataki na gyaran hali da sake gina rayuwar fursunoni.

A wani bangare kuma, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da daukar nauyin kudin rajistar WAEC da NECO na wadannan fursunoni.

Hukumar ta ce wannan mataki na nuna kudurin gwamnatin jihar wajen tallafa wa ilimi, karfafa matasa da kuma tabbatar da cewa wadanda aka gyara sun koma cikin al’umma a matsayin mutane nagari masu anfani.

Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya ta sake jaddada kudirinta na amfani da ilimi, horas da sana’o’i da hadin gwiwa wajen gina al’umma mai tsaro da ci gaba.

Allah Ya taimaki Najeriya.

🔴 GWAMNA BUNI YA TA’AZANTA WA IYALAN WANDA YA RASU A HATSARIN MOTA, YA ZIYARCI MASU JIKKATAYobe News ForumMai Girma Gwam...
15/05/2026

🔴 GWAMNA BUNI YA TA’AZANTA WA IYALAN WANDA YA RASU A HATSARIN MOTA, YA ZIYARCI MASU JIKKATA

Yobe News Forum

Mai Girma Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya bayyana alhininsa tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalan matashin da ya rasu sak**akon hatsarin mota da ya faru jiya.

Gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, tare da addu’ar Allah SWT Ya jikansa da rahama, Ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi.

A wani bangare na matakan da ya dauka nan take, Gwamna Buni ya kai ziyara Asibitin Koyarwa na Jihar Yobe domin duba wadanda s**a jikkata a hatsarin.

Yayin ziyarar, gwamnan ya gana da wadanda s**a samu raunuka tare da iyalansu, sannan ya samu karin bayani daga likitoci da ma’aikatan lafiya kan halin da marasa lafiyar ke ciki.

An shaida masa cewa wadanda s**a jikkata na samun kulawa mai kyau da gaggawa daga likitoci da sauran ma’aikatan asibitin.

Gwamnan ya yabawa shugabanci da ma’aikatan asibitin bisa saurin daukar mataki da kuma jajircewarsu wajen kula da marasa lafiya.

Haka kuma, ya tabbatar wa iyalan wadanda hatsarin ya shafa cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da mara musu baya tare da bibiyar lafiyar wadanda ke jinya har zuwa samun sauki.

Allah Ya jikkan mamacin, Ya bai wa wadanda s**a jikkata lafiya.

🔴 APC TA SAUYA RANAR ZABEN FIDDA GWANI NA MAJALISAR WAKILAIYobe News ForumJam’iyyar APC ta sanar da dage zaben fidda gwa...
14/05/2026

🔴 APC TA SAUYA RANAR ZABEN FIDDA GWANI NA MAJALISAR WAKILAI

Yobe News Forum

Jam’iyyar APC ta sanar da dage zaben fidda gwani na Majalisar Wakilai ta Tarayya domin babban zaben 2027 zuwa ranar Asabar, 16 ga watan Mayu, 2026.

A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar daga sakatariyarta ta kasa da ke Abuja, ta bayyana cewa sauran ranakun zabukan fidda gwani ba su canza ba.

Sabon jadawalin zabukan fidda gwani k**ar haka:

• Majalisar Wakilai ta Tarayya – Asabar, 16 ga Mayu, 2026
• Majalisar Dattawa – Litinin, 18 ga Mayu, 2026
• Majalisun Dokokin Jihohi – Laraba, 20 ga Mayu, 2026
• Zaben Gwamna – Alhamis, 21 ga Mayu, 2026
• Zaben Shugaban Kasa – Asabar, 23 ga Mayu, 2026

Sanarwar ta samu sa hannun Sakataren Yada Labarai na Kasa na APC, Felix Morka, CON.

Jam’iyyar ta bukaci mambobinta da masu ruwa da tsaki su lura da wannan sabon sauyi tare da ci gaba da shirye-shiryen zabukan fidda gwani.

Ku ci gaba da bibiyar Yobe News Forum domin samun sabbin labarai.

🔴 APC TA CE RANAKUNAN ZABEN FIDDA GWANI NA 2027 BA SU CANZA BAYobe News ForumJam’iyyar APC ta bayyana cewa ranakun da ak...
14/05/2026

🔴 APC TA CE RANAKUNAN ZABEN FIDDA GWANI NA 2027 BA SU CANZA BA

Yobe News Forum

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ranakun da aka tsara domin gudanar da zabukan fidda gwani na shekarar 2027 na nan yadda aka sanar tun farko, ba tare da wani sauyi ba.

A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar daga sakatariyarta ta kasa da ke Abuja, APC ta ce wannan karin haske ya zama dole bayan yaduwar rahotannin karya da rudani a kafafen sada zumunta da wasu hanyoyin sadarwa da ke ikirarin cewa an sauya ranakun.

Jam’iyyar ta bayyana jadawalin zabukan fidda gwani k**ar haka:

• Majalisar Wakilai ta Tarayya – Juma’a, 15 ga Mayu, 2026
• Majalisar Dattawa – Litinin, 18 ga Mayu, 2026
• Majalisar Dokokin Jiha – Laraba, 20 ga Mayu, 2026
• Zaben Gwamna – Alhamis, 21 ga Mayu, 2026
• Zaben Shugaban Kasa – Asabar, 23 ga Mayu, 2026

Sanarwar ta samu sa hannun Sakataren Yada Labarai na Kasa na APC, Felix Morka, CON.

Jam’iyyar ta bukaci mambobinta da jama’a su yi watsi da duk wani labari mara tushe tare da dogaro da bayanan hukuma kawai.

Ku ci gaba da bibiyar Yobe News Forum domin samun sahihan labarai.

Address

Tsalle Biyu Dogo Nini Ward Potiskum
Potiskum

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when YOBE News FORUM posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share