29/03/2024
JUMA,A TA UKU A CIKIN WATA MAI ALFARMA RAMADAN.
Kamar yau ne muka fara azumin watan Ramadan, yau gashi muna cikin juma,a ta uku a wannan wata mai alfarma, Ya ALLAH ka gafarta mana zunubanmu, ya Allah ka karbi dukkan ibadunmu, ya Allah ka sanyamu a cikin wadanda kakema gafara da rahama a cikin wannan wata Mai alfarma.
Yau gashi in mun kai azumine na 19 cif, kwanaki na wucewa, lokacinmu yana tafiya, muyi kokari Mu ribaci wannan damar da muka samu, Mai yiwuwane bama cikin wadanda zasuga azumin shekara Mai zuwa.
Ya Allah ka karba mana dukkan ibadunmu,
Yan,uwa Mu yawaita alkhairi da sadaka da kyauta da sada zumunci, da yawan salloli da karatun al,qur,ani.
Mu nace wajan rokon Allah musamman a lokacin da mukazo zamuyi buda baki, kafin musha Ruwa, ya tabbata Manzon Allah S .a.W yace ba,a juyar da addu,ar da Mai azumi yayita kafin Yayi buda baki,
Alla ka karba mana
Mahmud Ishaq Rano
Juma,a 19/Ramadan/1445.
29/march/2024.