27/07/2026
ZIYARAR JAMI'AR YUSUF MAI TAMA SULE DAKE KANO
Mai martaba sarkin Rano Amb Dr Alhaji Muhammad Isah Umar Autan Bawo na 19th Ya zauna a fada yau domin karbar gaisuwa.
Bayan zaman mai martaba sarki Jami'ar Yusif mai tama Sule sun kawo ziyara ga mai martaba sarki tare da neman sahalewar mai martaba sarki don sanin kaɗan daga cikin tarihin masarauta da kaɗe kaɗen Al'ada.
Sannan mai martaba sarki ya naɗa sabon dagacin garin chalbo dake kasar Kibiya.
Daga karshe mai martaba ya naɗa wasu fadawa kamar haka:
1.Alh Muhammad Hurdi Ciroman Shamaki
2.Nasiru Umar wakili Jakadan.
Allah ya taimaki sarki ya karawa sarki lafiya.
Rano Emirate Reporter's
27-7-2026