
12/08/2024
Nasiha ga saurayi da ya kai shekaru talatin (30).
1. 'Dan shekara talatin (30) ba yaro ba ne, in kana tsammanin har yanzu kai yaro ne to ka daina, kai saurayi ne da ya gama zangon farko na samartaka; kana mataki na biyu ne yanzu!
2. Ko ka san cewa ka kusa cika shekaru ashirin (20) da balaga? In haka ne, yana nufin kana da lada ko zunubi na kusan shekaru ashirin a rayuwarka.
3. Me ka cim ma a tsawon shekaru ashirin d'in nan! Ko ka san:
a. Ilimi: za ka iya kai wa ko wanne matakin ilimi a wannan shekarun; boko da addini, haddar ilimummuka da fahimtarsu, 'kwarewa a fannin da kake so!
b. Sana'a, za ka iya 'kwarewa a duk sana'ar da ka sa a gaba, kuma ka haifar da canji mai yawa ta hanyar 'kir'kira da amfanar da wasu cikin al'umma.
c. Manufa: a shekarun nan duk manufar da ka sa a gaba za ka iya cim mata, kuma ka yi fice cikinta tare da gogewa.
4.Ko ka san za ka iya zama uba ko kaka a wannan lokacin! , in ka yi aure kana da shekara sha hud'u, ka haihu kana sha biyar, zuwa yanzu 'yarka za ta iya kai wa sha biyar, kuma ta yi aure tana sha hud'u har ta haifa maka jika?
5. A shekarun nan za ka iya gina al'ummarka da abun da Allah ya ba ka na kowacce 'kwarewa da kake da ita, kuma ka kawo canji a kanka da al'ummarka.
6. To ka yi latti, kuma ba ka yi latti ba; ka yi latti in ba ka ribaci lokacinka ba, ba ka yi latti ba in ka duba kana da sauran jini a jika.
7. Ko ka san yanzu ne kake cikin ganiyar 'karfinka da 'kwarjininka? In haka ne, me ka shiryawa rayuwa mai zuwa? Mai kake tunani na jiya da yau da gobe?
8. Ko ka san a yanzu ya kamata ka yi nadamar abun da ya wuce, kuma ka yi tunanin gaba, sannan yanzu da kake karatun nan ya Kamata tunaninka ya canza?
9. Ko ka san irinku al'umma take nufi da samari su ne 'kashin bayan al'umma? To shin kai 'kashin ginawa ne ko rushewa?
10. To ka yi wa kanka karatun ta natsu, ka gyara, ka fuskanta, ka yi nadama, ka zauna da na gaba don kada ka fad'a kuskurensu, ka duba na baya don kada ka maimaita me ka aiwatar a lokacin da kake kamarsu!
Allah ya sa mu dace.