23/05/2025
Kamfanin Dangote Petroleum Refinery ya sanar da sabon saukin farashin lita na Man Fetur (Premium Motor Spirit – PMS) a fadin kasa.
Sabbin farashin sun bambanta daga ₦875 zuwa ₦905 kan kowace lita, dangane da wurin da ake siye.
Cikakken bayani kan sabon tsarin farashin ya nuna cewa: Lagos: ₦875, Kudu maso Yamma: ₦885, Arewa maso Gabas: ₦905, Arewa maso Yamma da Tsakiyar Najeriya: ₦895, Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas: ₦905.
Wannan yana nuna saukin farashi na ₦15 a kowace lita a dukkan yankuna da shagunan sayarwa da ke hadin gwiwa da kamfanin, ciki har da manyan kamfanonin sayar da man fetur irin su MRS, Ardova, Heyden, Optima Energy, Techno Oil, da Hyde Energy.
Kafin wannan sabon tsarin farashi, mazauna Lagos suna biyan ₦890 a kowace lita, yayin da farashin ya kai ₦920 a Arewa maso Gabas da yankin Kudu maso Kudu.
Yanzu, mazauna Lagos za su rika biyan ₦875, yayin da wadanda ke Arewa maso Gabas da Kudu maso Kudu za su biya ₦905 a kowace lita bisa sabon sauyin farashin.
“Man fetur da dizal dinmu suna da inganci sosai domin inganta aikin injin kuma ba su da illa ga muhalli,” in ji kamfanin a cikin sanarwar.