
05/12/2024
KU TAYANI YAƊA SAƘON NAN HAR YAKAI GA GWAMNAN JIGAWA.!
Tsarin bayar da bashin noma ga ma'aikata abu ne me kyau matuka da gaske,kasancewar duk ma'aikaci a hannun gwamnati yake,saboda ita take biyansa albashi,don haka kudinta ba zai salwanta ba irin yadda na anchor borrower da sauransu yake salwanta.don haka shawara ta anan ita ce;
1-Duk ma'aikacin da ze bukaci bashi a bashi,da sharadin idan mutum ya karba to ma'aikatan gona suke bi suna dubawa yadda za a tabbatar da cewa noman yayi.
2-Idan ma'aikaci ya karbi bashin ya ƙi yin noman to kai tsaye a tare albashinsa,kuma a doramasa tara har sai an gama cirewa sannan a ci gaba da bashi albashi.
3-Idan akayi noman to gwamnati ta karbi kayan noma a matsayin kudinta,ita kuma sai ta adana kayan a ƙarƙashin wasu amintattu yadda kayan ba zai salwanta ba.
4-Lokacin da kayan abinci yake tsada sai gwamnati ta fito da shi take sayarwa bisa farashi mai rahusa.
5-Lokacin da za a sayar din to ba za a sayarwa mutum fiye da kwano 2,3 zuwa 5 ba.
6-Idan aka samu wani dan kasuwa ya rabawa mutane kudi su sayomasa ya boye ko ya sayar da tsada to a hukunta masu zuwa sayen da wanda ya aikasu.
7-Babban al'amari a cikin wadannan shawarwari shine:
A SAMAR DA KAMFANONIN SARRAFA WASU DAGA CIKIN IRIN WADANNAN KAYAN NOMA,KAMAR KAMFANIN SARRAFA ALKAMA,GYADA,DA RAKE.
Kamfanin alkama zai yi fulawa,taliya,makaroni,semovita,dusar dabbobi,abincin kaji d.s.
Kanfanin gyada ze samar da mai,ƙuli-ƙuli,malkaɗaɗɗiyar gyaɗa,ɓawon gyadar kuma a hada abincin dabbobi ko makamashi.
Kamfanin rake in ma ba sugar ba to a ke yin mazarkwaila.
Da haka noma zai bunkasa,talakan ƙauye zai samu aiki a gona,kamfanin zai dauki ma'aikata,jiha za ta samu kudin shiga,talaka zai sayi abinci da sauƙi,shugaban da ya kawo wannan tsarin zai samu lada da sauran fa'idoji da ba za su taƙaitu ba.!
LOKACI YAYI DA DOLE MU SAN INDA MUKA DOSA TUN KAFIN DARE YA YI MANA.!!!
Allah yasa saqo na yaje inda ya kamata.!!!
Muhammad Sulaiman Ringim