16/07/2023
Mutuwar Sarki Yazid
Ga dukkan alamu Yazidu ya bar duniya da juyayin
abu guda daya da yake fargaban gamuwa da
Allah a kan sa. Wannan lamarin kuwa shine kisan
Husaini da danginsa. An fadi cewa, karshen
kalaman da ya furta a duniya su ne: “Ya Allah!
kada ka rike ni da abinda ban so ba kuma ban
bada umurni ba. Ya Allah! Kayi hukunci a tsakani
na da Ibnu Ziyad – yana nufin gwamnansa na
Kufa wanda ya sa aka kashe Husain. Yazid ya
rasu a ranar 14 ga Rabi’ Awwal na shekarar 64H.
Duka duka mulkinsa bai cika shekaru hudu ba
amma al’ummar musulmi ta samu ja da baya
matuka daga karfinta da kwarjininta a cikin
wannan bakin lokaci. Rundunar Husain bin
Numair wacce take tsare da Ibnuz Zubair da
jama’arsa suna dako a wajen Makka ba su samu
labarin mutuwar Yazid ba sai bayan sati uku cur.
Abu kadan ya rage wannan runduna ta hada kai
da Ibnuz Zubair bayan sun samu wannan labari.
Amma abinda ya kawo cikas shi Bin Numair ya
nemi ya dora hannunsa a kan na Ibnuz Zubair ya
yi masa mubaya’a da sharadin a yafe duk
jinainan da s**a gudana a baya. Ya ce kuma idan
an yi haka na lamunce ma kasar Sham gaba
daya zan sa su yi maka mubaya’a. Shi kuma sai
ya ki karbar wannan sharadi. A nan ne Bin
Numair ya juya yana nadama, ya ce, “Dubi yadda
nake kiran sa zuwa sarauta yana neman ci gaba
da fitina”. Ashe dai Allah bai kaddare shi da
zama sarki ba. A can kuma birnin Dimashka ta
Sham an sha takaddama sosai a kan wa za a
nada bayan Yazidu tun da shi bai bar wani wasici
a kai ba. Daga bisani sai aka dora wa dansa
Mu’awiyah karami jan wannan ragama. Amma
ina dadin mulki a lokacin tashin hankali! Ba da
jimawa ba shi wannan sai ya yi murabus ya bar
wuri wayam ana ta muhawara ba mai bukata. A
nan ne Umawiyyawa s**a bukaci su je su
sasanta da Ibnuz Zubair a Makka, su yi masa
mubaya’a daga bisani kuma sai Allah ya sa aka
jitu a kan Marwan bin Al Hakam wanda shi ne
mulki ya ci gaba a cikin zuriyarsa. Matsayin
Malaman Sunna A Kan Wadannan Fitinu
Annabinmu Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam
ya sanar da cewa fitinu zasu gudana a bayansa.
Kuma ya fadi cewa alherinka yana gwargwadon
nisantarka daga gare su. Wadannan hadisai suna
na a shimfide cikin littafan Sunna a Kitabul Fitan
na kowane littafi. Duba alal misali: Sahihul
Bukhari, Kitabul Fitan, Babun takunu fitnatun al
qa’idu fi ha khairun minal qa’im, Hadisi na 6670.
Game da abinda ya faru a Karbala, ba wani
sabani a tsakanin malamai cewa, an tafka barna
wadda ba ta dace ba. Abin takaici ne da ya nuna
cewa ba a mutunta Manzon Allah ba a cikin
sha’anin iyalinsa. Wanda kuwa duk yake da
hannu a ciki to, ba abinda zai hana shi gamuwa
da fushin Allah in ba tuba ya yi ba tuba
ingatacciya. Amma a game da wa ke da alhakin
wannan ta’asa, to kowa ya fadi albarkacin
bakinsa. Duk wanda yake da kyakkyawan nazari
da sa adalci cikin hukunci zai iya lura da cewa
kaddarar Allah ita ce babban jigon abinda ya
faru. Kuma duk abinda ka ga Allah ya yi to,
tabbas akwai hikima a cikinsa, ko mun san ta ko
bamu sani ba. Hasashen da Ibnu Taimiyyah ya yi
a nan abin sauraro ne matuka. Ga abinda ya ce:
Hasan da Husaini sun rayu a cikin kuruciya
zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam. Don haka ba su samu damar taimaka
masa ba a wajen jihadi da yada kalmar Allah
kamar yadda sauran sahabbai s**a yi. (A
Lokacin wafatin Manzon Allah, Hasan yana da
shekaru bakwai ne da wata tara, a yayin da
Husaini yake da shekaru shida da watanni
takwas). Duk wahalhalun da sahabbai s**a sha a
Makka da tsangwama da tashin hankali, haka ma
duk gwagwarmayar da s**a yi bayan sun bar
gidajensu da yakokan duk da aka yi; Badar da
Uhud da Khandak da Tabuk da sauransu inda
Allah ya yi ta rabon darajoji da gafara ga
sahabbai su wadannan bayin Allah ba su samu
kasancewa a ciki ba. Kasancewar Allah ya zaba
masu wani babban matsayi a aljanna ya sa Allah
ya jarabce su da wata jarabawa a irin nasu
matsayi kuma ya basu shahada. Don haka ma
Ibnu Taimiyyah ya kara da cewa, kashedinka ka
zargi Husaini a kan fitowar da ya yi bayan duk
shawarwarin da aka ba shi. Ka sani Allah ne
yake ingiza shi zuwa ga daukaka da darajar da
ya hukunta masa. Duba Minhajus Sunnatin
Nabawiyyah na Ibnu Taimiyyah (4/527-536).
Digital creator