24/07/2023
KOTU ZAMA NA BAKWAI DA TAKWAS.
A jiya Lahadi 23/07/2023 kotun Sauraron Kararrakin za'ben Gomna a Jahar Adamawa tayi zama na musamman. Zaman Wanda ya gudana da misalin karfe 12:40 ya karbi bakoncin Barrister Hudu Yunusa Ari Shugaban Hukumar za'be na Jahar Adamawa Wanda aka dakatar
Hudu ya Isa harabar kotun a cikin tsauraran matakan tsaro domin shaidawa kotun abinda ya gudana a za'ben na Gomna.
Tun farko dai Lawyan Gomna Fintiri ya shaidawa kotun cewa su basu yarda Hudu ya bada shaida ba a dalilin haka kotun kada ta amince da Hudu a matsayin shaida.
Amma a nashi bangaren Lawyan Sanata Binani ya nuna mamaki matuka akan wannan matsaya ta Fintiri. Olujinmi SAN ya ce waye ya cancanci bada shaida bayan wanda ya gudanar da za'ben Gomna a Jahar Adamawa. Olujinmi SAN ya shaidawa kotun idan dai ba tsoron Hudu sukeyi ba toh su barshi ya bada shaidar abinda ya sani.
An yi zazzafan muhawara akan ko Hudu zai bada shaida ko ko? Wannan muhawara aka tayi har lokacin tashin zaman kotun inda kotun ta ce a dawo gaban ta yau litinin.
Daga bisani sai Hudu ya tabbatar ya baiwa registry duk takardun da yako wato domin ayi filing domin alkalan su duba.
A zaman kotun na Yau Barrister Olujimi SAN ya shaidawa kotun cewa duba da wasu al'amura da ke kaiwa komo musamman ma a bangaren tabbatar da tsaron Hudu da Kuma hujjojin da aka gabatar, ya janye sa ke dawo da Hudu a gaban kotun. Olujinmi ya Kara da cewa, hojjojin da s**a gabatar wa kotun sun Kai mizanin da suke bukata batare da Karin shaidu ba.
Bayan Hudu Yunusa Ari sai Kuma shaida na gaba da Sanata Binani ta gabatar. Wannan shine "star witness" na Binani Wanda yafi kowane shaida muhimmanci. Shi kuwa masani ne na harkokin za'be Wanda ya zo gaban kotu ta d'imbin takardu Wanda ya ke nunawa a fili kuri'un da Sanata Binani ta samu a za'ben Gomna a Jahar Adamawa Wanda ya d'ara na Wanda ke ikirarin ya ci za'ben.
Shaidan Wanda shima an Kai ruwa rana da Lawyoyin Fintiri kamin su barshi ya bada shaida. Nan ma kotun ta Yi amfani da karfinta