30/05/2026
Mutum Uku Sun Mutu a sakamakon fadawa Rijiyoyi Daban-daban a Kano
KatsinaTimes
Mutane uku, ciki har da wata mata da ƙaramin ɗanta, sun rasa rayukansu sakamakon faɗawa rijiyoyi a wasu yankuna daban-daban na Jihar Kano, kamar yadda Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar.
Mai magana da yawun hukumar, Saminu Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
A cewarsa, lamarin farko ya faru ne a yankin Semegu da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso, inda wani mutum da ba a tantance sunansa ba ya faɗa cikin rijiya ya mutu.
Ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 7:06 na safe daga wani mai suna Hafizu Garba-Saminu, wanda ya sanar da su aukuwar lamarin.
“Nan take muka tura jami’an ceto zuwa wurin, inda s**a fito da gawar mutumin daga cikin rijiyar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa an miƙa gawar ga jami’in binciken manyan laifuka na ofishin ‘yan sanda na Panshekara, Salisu Salihu, domin ci gaba da bincike.
A wani lamari na daban kuma, wata mata mai shekaru 32 mai suna Maimuna Sh*tu tare da ɗanta mai watanni 18, Harisu Muntari, sun mutu bayan sun faɗa cikin rijiya a ƙauyen Madarin Taba da ke Ƙaramar Hukumar Warawa.
Abdullahi ya ce hukumar ta samu wani kiran gaggawa da misalin ƙarfe 9:40 na safe daga wani Buhari Sa’idu, wanda ya sanar da cewa wata mata da ɗanta sun faɗa cikin rijiya.
Ya bayyana cewa an tura jami’an ceto cikin gaggawa zuwa wurin, inda aka fito da gawarwakin mutanen biyu daga cikin rijiyar.
A cewarsa, an miƙa gawarwakin ga shugaban unguwa, Yusuf Surajo, da kuma mijin matar, Muhammad Sh*tu.
Hukumar kashe gobarar ta ce ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin aukuwar hadurran.
Sai dai hukumar ta yi kira ga al’umma musamman iyaye da masu kula da yara da su tabbatar an rufe rijiyoyi yadda ya kamata domin kauce wa irin waɗannan munanan haɗurra.