
20/08/2025
Ita Mace, In Tana Shekaru 16-21, Kamar Ƙwallon Ƙafa (Football ⚽) Take Kan Farin Jini, Mutum 22 A Fili, Kowa Na So Ya Nuna Bajintarshi Don Ya Sami Nasara. Ita Kaɗai, Suna Ta Rubibinta.
In Mace Takai Shekara 22-25 Sai Ta Koma Kamar Ƙwallon Kwando (Basket Ball 🏀). Mutun Goma Ne Ke Gasar Nuna Bajinta Akanta. Mai Rabo Ya Samu.
Daga Shekaru 26-30, Sai Ta Koma Kamar Ƙwallon Tebur (Table Tennis 🎾). Mutum Biyu Ne Ke Fafatawa. Tsakaninsu Wanda Yayi Nasara Ba Wata Murnar Kirki Yake Ba.
In Shekarunta Sun Ka Kai 31-35 Kuwa, Kamar Ƙwallon (Gora Golf ⛳) Take Komawa. Mutum Ɗaya Yake Buga A Barsa, In Ta Faɗa Rami Ya Ɗauko In Ma Ta Wuce Ya Ɗauko. Shi Yake Fama Shika Ɗai Ana Kallonshi.
A Nan, Ne In Abubuwa Ba Su Tafi Yanda Ake So Ba, Sai Ta Koma Yar Kungiyar Kare Haƙƙin Mata Da Yara. 😅
A Shiga Rediyo Ana Zagin Mazaje Ana H**e Kunnen Matan Da Allah Ya Sa Haƙonsu Ya Cimma Ruwa Suke Tsugune Gidan Mazajensu.
Allah Ya Kyauta 🙏