02/08/2026
AN KAWO ƘARSHEN TATTAKIN ARBA'IN NA YANKIN PAMBEGUWA A GARIN MAIGANA
Bayan ɗaukar tsawon kwanaki uku ana gabatar da Tattakin Arba'een na Yankin Pambegua wanda aka fara daga ranar Juma'a, zuwa yau Lahadi, 02/08/2026, an rufe taron a garin Maigana dake karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna, inda Sheikh Ahmad Yusuf Yashi ya gatabar da jawabin rufewa.
Da ya ke jawabin, Wakilin 'yan'uwa Musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Yaƙub Zakzaky (H) na Da'irar Bauchi, Sheikh Ahmad Yusuf Yashi, wanda shi ke jagorantar yankin, ya fara ne da godiya ga Allah (T) bisa ni'imar kammala wannan taro lafiya, tare da taya yan'uwa Musulmi ta'aziyya na rashin jikan Manzon Allah (S), wato Imam Hussaini (AS).
Sheikh Ahmad Yashi ya bayyana cewar a shekarar da ta wuce an rufe Tattaki a Soba, bana kuma an yada zango Maigana, sai ya ce "shekara mai zuwa muna sa rai idan Allah ya yarda mu dangana da birnin Mujaddadi (Zaria garin Sayyid Zakzaky)."
Da ya ke magana game da al'amarin fitowar Imamu Hussain (AS) zuwa Karbala, Sheikh Yashi ya bayyana cewar 'yan'uwa da aminai duka sun kewaye Imam Hussain (AS) suna cewa me zai sa ya fita a wannan lokaci tare da iyalai gaba ɗaya.
Sai Sheikh ya kawo amsar da Imam ya basu da cewa: "Ban fito domin shishshigi ko neman matsayi ko don zalunci ko don ɓarna a doron kasa ba; abunda ya sa na fito shi ne don kawo gyara a cikin addinin kakana (Muhammad) ta hanyar umurni da kyakkyawa da hani da mummuna.
Sai Sheikh ya sake ruwaito inda wasu suke cewa: "Wurin da za ka kai iyalanka halaka ne." Sai Imam ya ce "Allah ya ga daman ya ganni an kashe ni, iyalai na kuma a matsayin ribatattun yaƙi."
Sheikh Yashi ya ƙara da cewa, idan ka duba shahadar Imam Hussain (AS), al'amari ne mai girma, amma idan aka duba cewar Allah ya ɗaura musu wannan mas'uliya na jagoranci ne domin su zamo fansa ga al'ummarsu.
Game da sadaukarwar Imam Hussain, Sheikh Yashi ya ce "shi ne ya raya addinin nan. Saboda haka babban darasin da shahadarsa ke koyar da mu shi ne raya addini, domin shahadarsa ne take baiwa duk wani mai addini kariya."
Sheikh Yashi ya ci gaba da bayyana cewar a yau da an rasa mutane tsayayyu irin na Iran waɗanda da'awar Imam Hussain ne s**a samar da su, da yau al'ummar musulmi ba su da wasu masu tsayuwa a kan al'amarinsu.
Yau wani ya yi kaɗan ya nuna yatsa ma Jamhuriyar Musulunci (ta Iran), tun ma kafin ta zamo kamar haka, ballantana kuma lokacin da ta yi karfi kamar yanzu. Babu wata ƙasa a duniya da ta kai Iran ƙarfi, kamar yadda ya ruwaito zancen wani mai sharhi a kan lamurran yau da kullum.
Game da Sayyid Ibraheem Zakzaky da waɗanda Malamin ya bayyana a matsayin masu shirin ganin bayansa, ya ce: "Jagora (Sayyid Zakzaky) dashen Allah ne, nan gani nan bari!" Sannan ya fayyace cewar shi Jagora ya ce taken taron bana shi ne "Tafarkin Imam Hussain (AS) mafita ga wannan al'umma" sai ya bayyana cewar wajibi ne idan al'umma suna son ci gaba a rayuwa mai 'yanci su koma kan wannan tafarki.
A ƙarshe Sheikh Muhammad Abbare Gombe ne ya rufe taron da addu'a.
©️ Media Forum – Pambeguwa Axis
19-Safar1448 02/08/2026