14/06/2025
📝 Rikicin Tsaro a Najeriya: Lokaci Yayi daya kamata Mu Farka daga Barci
Wani abu mai ban takaici da damuwa shine yawan mutanen da ake kashewa da kuma sacewa a Najeriya — musamman a watan Mayun da ya gabata. Kididdiga ya nuna cewa mutane 1,296 sun rasa rayukansu, sannan an yi garkuwa da mutane 1,086 a faɗin ƙasar nan. Wannan ba wata lissafi ce kawai ba — waɗannan rayuka ne. Iyaye ne, ƴaƴa ne, matasa,yara da tsofaffi ne da ba su da laifi.
Wani abin mamaki shine yadda muke cigaba da rayuwa kamar ba komai ya faru. A wasu ƙasashe, kisan mutane biyu ko uku na iya girgiza ƙasar. Amma a nan? Sau da yawa muna cigaba da dandalin siyasa da shirme a kafafen sada zumunta — kamar muna rayuwa a wata ƙasa dabam.
Ina tambayar kaina da sauran ƴan uwana ƴan Najeriya: Yaushe za mu ɗauki wannan matsala da muhimmanci? Yaushe gwamnati za ta daina ɗaura laifi kawai ga masu tada ƙayar baya, har ta duba matsalolin da ke haifar da su — kamar talauci, rashin aikin, rashin yi, ilimi, da rashin adalci?
Babu wani abu da ya fi raba ƙasa da tabbatar da rashin gaskiya irin yadda ake kallo rayuwar ɗan Adam a matsayin lamba kawai. Dole ne mu farka daga barcin da muke ciki. Idan har gwamnati ba za ta iya kare rayukan al’umma ba, to me ya rage mata?
Ba wai kawai mu na so a daina kashe mutane ba ne. Mu na so mu ga ƙasa mai gaskiya, mai adalci, wacce kowa zai ji daɗin zama a cikinta. Najeriya tana da albarka — amma tana cikin wahala, saboda gazawar shugabanni da shirun da talakawa ke yi.
Yanzu lokaci ne da ya dace mu daina ɗaukar labarin kashe-kashe da garkuwa da mutane a matsayin sabon “ƙari” na kullum. Mu daina watsi da labarai masu ɓata rai da sauƙin zuciya. Rayuka na salwanta, kuma shiru tamkar yarda ne.
"Ka tuna, shiru a gaban zalunci ba zaman lafiya ba ne — haɗin kai ne da zalunci."