08/02/2022
Yadda Zaka Karawa Computer Dinka Sauri..
Wani lokaci kanason aiki cikin sauri to amma Computer din naka bata sauri, musamman ma idan karama ce, gashi kuma kanaso kayi wani aiki kila ma budurwarka ce ta baka aikin, kuma bakaso aji kunya..😁 wanda hakan yasa dole sai kasiya karin "RAM" na Computer din sannan zata kara sauri..
To insha Allah ga wata hanya wadda basai kasiya "RAM" ba Computer dinka zata qara sauri kayi abinda kakeso kayi cikin yan lukutta kalilan..
Matakin farko dai kayi bissimillah sannan kaje kai tsaye cikin computer dinka wurin kan "Desktop Icon" da aka rubuta kalmar "Computer" kokuma kawai ka taba Key din Computer mai alamar Window a hade da "E" Misali; "Window+E" to zakaga wajen "Hard Disc" din Computer din ya bude.
Mataki na biyu; Bayan ka bude wajen "Hard Disk" din sai kayi "Right Click" kaje daga kasa wajen "Properties" sai kashiga, bayan kashiga sai kaje wurin da aka rubuta "Advanced System Settings" zaka ganshi gefen hagu daga sama sai kawai kashiga...
Bayan ya bude zai kawo maka zabi da yawa sai ka zabi "Advance" idan kuma yana a sama shikenan.
Mataki na ukku; bayan ya bude sai kayi kasa kadan zakaga "Performance" daga gefen damansa akwai wurin da aka rubuta "Settings" sai kashiga, bayan ya bude sai kasake zabar "Advanced" daganan zakaga rubutu guda biyu daya a sama daya a kasa sai ka zabi "Program" a na saman, shikuma na kasan se ka taba wurin da aka rubuta "Change" bayan ya bude a farko zakaga wurin da aka rubuta "Automatic" to sai ka taba a alamar Good din wajen fita, daganan sai kayi kasa kadan ka zabi "Customs" size: filin saman se kaje wajen "Recommended" zaka ganshi daga cen kasa sai kayi Copying Numbers din da s**a fi na filin farkon da kadan sai ka saka a wajen, Daganan sai kataba "Ok" kabi duk windows din da kabude ka rufesu, daganan sai ka kashe Computer din sannan kasake kunna ta..
Shikenan dan'uwa kagama kuma ka karawa Computer dinka saurin yin ayyuka zakaga sauyi wajen saurin aiki zakaga tafi yadda take farko