
31/07/2025
A wani yunkuri na karfafa gwiwar manomanmu da sake farfado da harkar noma a yankin mu na Sokoto ta Gabas, mun kaddamar da rabon taki kyauta ga manoman yankinmu na Sokoto ta Gabas da nake wakilta, a yau Alhamis.
Dukkanin kananan hukumomi takwas na yankinmu Sokoto ta Gabas da nake wakilta za su ci gajiyar wannan takin cikin tsanaki wanda ya hada da sarakunan Jihar Sokoto reshen Sokoto ta Gabas, kungiyoyin kwadago, kungiyoyin addinai, hukumomin tsaro, tare da sauran al’ummar wannan yanki.
Masu ruwa da tsaki ga harkokin siyasarmu da s**a yi jawabi a madadina a wajen taron kaddamar da rabon takin karkashin jagorancin babban wakilina Alh Kabir Sarkin Fulani, sun yabawa jagorancin mu kan wannan shiri, inda s**a bayyana cewa wannan ne karon farko da ake baiwa manoma takin zamani kyauta, inda s**a ce hakan zai taimaka wajen bunkasa harkar noma da kuma samar da wadataccen abinci a yankin Gabascin Sokoto.
Shirin takin zamani kyauta da muka kaddamar a yau ya nuna karara da tsayin daka wajen karfafa gwiwar manomanmu da sake farfado da fannin noma yankin Sokoto ta Gabas.
Noma ba kawai kashin bayan tattalin arzikin yankinmu ba ne, har ma yana da matukar muhimmanci ga ci gaban jiharmu da ci gaban kasarmu baki daya.
Wadannan tsare-tsare wani bangare ne na dabarun mu na inganta noma, inganta ababen more rayuwa, da tallafawa manomanmu. Don haka ina kira ga manoman mu da su yi amfani da wadannan takin cikin gaskiya da inganci. Muna da kwarin gwiwar cewa wadannan matakan za su kara yawan amfanin gonakin da muke noma da kuma karfafa samar da abinci a jihar Sokoto musamman al’ummarmu na Sokoto ta Gabas baki daya.-SIL.