18/09/2026
Atiku ga Tinubu: A rage farashin mai, a bar ’yan Najeriya su shaƙa
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta rage farashin man fetur domin rage wa ’yan Najeriya raɗaɗin tsadar rayuwa.
Atiku ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a Abuja, yayin da yake magana kan farashin man fetur, matakan rage radadin rayuwa da kuma halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.
Ya ce cire tallafin man fetur ya ƙara tsadar sufuri, wanda hakan ke haifar da hauhawar farashin abinci da kuma ƙarin kuɗin gudanar da noma, kasuwanci da sauran harkokin tattalin arziki.
A cewarsa, manoma na kashe kuɗi mai yawa wajen jigilar amfanin gonakinsu, yayin da ’yan kasuwa ke fuskantar tsadar safarar kaya, ma’aikata kuma ke kashe ƙarin kuɗi wajen zirga-zirga zuwa wuraren aikinsu.
Atiku ya soki dogaro da tallafi kawai, yana mai cewa: “Tallafi na rage zafi ne kawai, amma ingantacciyar manufa tana magance tushen matsalar.”
Ya kuma gargadi gwamnatin Tinubu da kada ta maimaita abin da ya ce ya faru wajen cire tallafin man fetur a batun tallafin wutar lantarki, musamman ganin shirin kawo ƙarshen tallafin wutar lantarki daga shekarar 2027.
Atiku ya ce idan aka zaɓe shi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, zai samar da tsarin tallafin man fetur da aka tace a Najeriya, wanda zai kasance ƙarƙashin iyakacin kashe kuɗi, amincewar Majalisar Dokoki ta Ƙasa da kuma binciken masu zaman kansu.
Ya ce manufar za ta ƙarfafa tace man fetur a cikin gida tare da rage farashin da masu amfani za su biya.
Atiku ya kuma bayyana cewa a shirye yake ya bai wa gwamnatin Tinubu shawarwarin tsarin da zai taimaka wajen rage farashin mai, ko da kuwa gwamnati za ta sauya sunan shirin kuma ta ɗauki yabo.
“Abin da ya fi muhimmanci a gare ni shi ne ’yan Najeriya su biya kuɗi kaɗan,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ci gaban tattalin arziki ya k**ata ya bayyana a cikin gidajen ’yan Najeriya, kasuwanni da ƙarfin sayen ma’aikata, ba wai kawai a ƙarin kuɗaɗen shiga na gwamnati ko alkaluman GDP ba.
Atiku ya ce yana shirye ya fafata da Tinubu a siyasa, amma ba zai taɓa yin takara da jin daɗin al’ummar Najeriya ba.