03/11/2025                                                                            
                                    
                                                                            
                                            ZAA DENA AMFANI DA DOLLAR AMERIKA A SIYEN TICKETS A NIGERIA....
Gwamnatin Nigeria tana duba yiyuwar dakatar da siyen tikitin jiragen saman kasashen waje da akeyi da Dollar...
A yanzu kusan duk Tickets da ake siya na kamfanonin jiragen sama da suke jigilar fasinjojin Nigeria suna siyar da Tickets dinsu ne da Dollar maimakon Naira wanda hakan ke karawa Dollar daraja a Nigeria kuma yake rage darajar Naira, sai dai a iya cewa hakan na gaf da zama tarihi domin gwamnatin Nigeria tace hakan ba zai cigaba da faruwa a kasarta ba..
Kamfanonin jiragen sama irinsu British Airway, Lufthansa da Emirates suna siyar da Tickets dinsu da Dollar maimakon Naira duk da cewa fasinjojin Nigeria suke dauka a cikin Nigeria, akwai sauran kamfanoni masu yawa da suma suke siyar da Tickets da Dollar maimakon Naira ..
Gwamnati tace dole ne ta kawo tsare tsaren da zasu durkusar da Dollar tare da hanata cigaba da hauhawa....
Yadda Dolar take a matsayin kudi haka ita ma Naira take don haka dole ne a mutumta Naira a cikin Nigeria, ba zai yiyu aki amfami da Naira a Amurka sannan ace zaa dinga amfani da Dollar a Nigeria....