22/08/2024
LAIFIN DA SARKIN GOBIR YAYI AKA KASHE SHI
Daga Datty Assalafy
Gwamnatin jihar Sokoto ne ta kira taro kan sha'anin tsaro (security council meeting) wanda ya hada da manyan Sarakuna na jihar
Bayan kammala taro kan tsaro, an umarci Sarkin Gobir akan ya sanya hannu a takarda ya amince fulanin daji su dawo cikin gari, wai za'ayi sulhu
Shi kuma Sarkin Gobir yace gaskiya ba zai iya saka hannu ba, domin baya so ace shine yayi sanadin dawowar barayin daji cikin gari wadanda akace wai sun tuba, yace shi bai san da wani ido zai kalli al'ummarsa ba idan haka ta faru
Yace amma duk da haka shi bai da ikon ya hana Gwamnati aiwatar da abinda take so, amma dai shi ba da sa hannunsa ba
To bayan kammala taron ne akan hanyarsa na dawowa aka tura barayin dajin s**a kamashi tare da yaransa, wanda daga karshe s**a kashe shi, da ma shi din ake son kashewa saboda bai bada hadin kai aci amanar mutanen sa ba, don haka kisan sa ba komai bane face siyasa
Duk wulakancin duniyar nan da azabtar wa sun masa, yayi ta kuka yana rokon Gwamnatin jiha ta taimaka masa gashi bai da lafiya ga tsufa amma Gwamnati tayi biris da shi
Haka nan babu wani bayani na agaji gareshi daga Sarkin Musulmi b***e sauran takwarorinsa manyan Sarakuna masu daraja ta daya irin nasa, duk sun yi watsi dashi, wai a hakan sune suke wakiltar Musulunci a yankin Arewa
Ni dai ban ga wani abinda ya rage mana ba, yaki kam an gama cinye mu da shi, siyasar Demokaradiyya ta lalata komai, babu wani abu mai mutunci da daraja da ya rage mana
Dole mu tashi mu nemi mafita, 'yan siyasa ba zasu iya ba, sunci amanarmu, Sarakunanmu ba zasu iya ba saboda tsoron kujeran mulkinsu, Malamai ba zasu iya ba domin wasu daga cikinsu da ake jin muryansu sunci amana, sun karbi kudi sun sayar damu a hannun miyagu
Allah Ka tausaya mana, Ka bamu mafita na alheri.