03/08/2026
GROWTH LAB PROGRAMME!!!
An buɗe neman masu shiga Growth Lab, wani shiri na horo da bunƙasa kasuwanci na tsawon makonni 12 ga fasahohin kasuwanci (Tech Startups) da s**a wuce matakin MVP, waɗanda matasa 'yan Najeriya masu shekaru 18 zuwa 35 s**a kafa.
Shirin yana ƙarƙashin Bankin Masana'antu (BOI) ta hanyar iDICE Programme, kuma yana ba da tallafin kuɗi, horaswa, jagoranci (Mentorship), da kuma shirya masu kasuwanci domin samun jari da faɗaɗa kasuwancinsu.
Abubuwan da zaɓaɓɓun mahalarta za su samu:
-Zuba jari har zuwa $100,000
-Horo kan yadda ake shirya kasuwanci domin samun masu saka jari, tare da jagorancin ƙwararru
-Damar samun ƙarin tallafi har zuwa $250,000 idan an cimma ƙa'idodin ci gaban kasuwanci.
Idan kana da Tech Startup mai sabbin dabaru a Najeriya, wannan babbar dama ce ta bunƙasa kasuwancinka.
Shida Loan Na BOI INIDE Daban Daban ne Ba Daya Bane
Link ɗin yin rajista
Yana Comment Section
Ku kasance tare da mu domin samun sahihan bayanai kan duk wata dama da shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya da sauran tallafin kasuwanci