18/10/2025
ILIMI KOGI NE: "Sufaye ne s**a yaɗa Musulunci kuma s**a ɗaga tutarta. Jarumtakar su da gudun duniyarsu ita ta tsaya wa ƙwarjinin Musulmai; kyakkyawan ɗabi'unsu yasa Musulmi suke da farin jini.
Goni Yusuf Rabiu ya ambaci manya daga cikin mujahidai a ƙasar Afirka, kamar haka: "Kaɗan daga cikin sufayen da s**a yi yaƙi da Turawan mulkiya don kare Musulunci daga sharri (Christian) mission kuma s**a jaddada Musulunci a Afirka.
Sheikh Usman ɗan Fodio a Nigeria da Niger — Sufi
Sheikh Umar al-Futi a Mali da Burkina, Cameroon — Sufi
Mujahid Umar Mukhtar a Libya — Sufi
Abdulkareem bin Jaami'i a Chad — Sufi
Muhammad al-Mahdi a Sudan — Sufi
Samori Touré a Guinea — Sufi
Muhammad Abduh (Egypt) — Sufi
Ahmed Bey (Algeria) — Sufi
Abu Amamah da Ahmed Bey a Tunisia.
Daga ƙarshe, ko kun san Ismaa'il Haniyarh, shugaban Hæmãss na Falasɗinu, masu yaki da Isra'ila, shi ma Sufi ne, ɗan gidan Sufaye?
Tambaya: Me yasa babu wanda yake yaƙar Turawa da kafirai sai Sufaye? Mene ne sirrin?"
Amsa: Ƙaunar Manzon Allah (SAW) da yawan zikrin La ilaha illallah itace sirrin.
—Cewar Amb. Sheikh Nasir Ado Musa