07/05/2025
YANZU-YANZU: Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya kalubalanci Shugaban kasa Bola Tinubu, da ya sauya motocinsa da sauran motocin da fadar Gwamnati ke hawa da ƙirar Najeriya.
Atiku ya kalubalanci Tinubu ne biyo bayan wata sanarwa da Ministan yada labarai Muhammad Idris, ya fitar akan haramta shigo da kayayyaki na kasashen waje a Najeriya.
A cewar Atiku ya k**ata Tinubu idan har da gaske yake na habaka tattalin arziƙin Najeriya, ya k**ata ya sauya motocinsa da ƙirar kamfanonin Innoson, Nord da sauransu.
A ranar Litinin, Majalisar Zartarwa ta Kasa (FEC) ta amince da wani sabon tsarin “Nigeria First” da ke baiwa kayan da aka samar a gida fifiko a duk wani tsarin siye da siyarwa na gwamnati.
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai ga Al’umma, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan bayan taron FEC da aka gudanar a Abuja, inda ya ce za a karfafa wannan doka ta hanyar umarnin shugaban kasa.