10/12/2025
YANZU-YANZU: Ɗarikan Tijjaniyya Da Kadiriyya a Jihar Kaduna Sunyi Allah Wadai Akan Ban Garancin Gwamnatin Jihar Kaduna Da Ofishin Sifikan Nigeria Su Ke Yi Musu ~Imam Dr. Hamza Assudaniy Zariya...
Sakataran Majalisan Malamai Ta Tijjaniyya, Imam Hamza Assudaniy, Shine Ya Bayyana Haka, Yana Me Allah Wadai Da Nuna Ko In Kula Da Gwamnatin Jihar Kaduna Da Speaker Mai Wakiltar Karamar Hukumar Zariya Ta Jihar Kaduna...
Assudaniy Yace, 'Yan Darikun Sufaye Tijjaniyya Da Kadiriyya Musamman a Jihar Kaduna Sunyi Allah Wadai Da Irin Mu'amalan Da Ake Musu Da Mayar Dasu Saniyar Ware Daga Ofishin Gwamnatin Jihar Kaduna Da Ofishin Sifikan Nigeria, Mai Wakiltan Karamar Hukumar Zariya...
Ya Kara Da Cewa, Ba'a Gudanar Da Harkokin Addinin Musulunci Dasu Yadda Ya Kamata, Kuma Babu Wani Abu Na Gani Na Fada Da Akeyi Da Yan Tijjaniyya Ko Kadiriyya A Jihar Kaduna...
An Baiwa Wasu Yan Uwan Mu 'Yan Kungiyar Izala Ingantattun Muk**ai Na Gani Na Fada A Cikin Gwamnati, Amma Tijjaniwa Da Kadirawa Basu San Matsayar Su Ba a Gwamnatin Jihar Kaduna Da Ofishin Sifikan Nigeria...
Don Haka Suna Kara Sanar Da Gwamnati Akan Cewa, Suna Sane Da Abinda Ake Yi Musu A Cikin Gwamnati, Kuma Akwai Ranar Kin Dillanci....