
14/08/2023
Facebook sun fitar da sabon tsarin da zaka biya kudi, suyi maka Verified din account dinka na Facebook.
A shekarun baya Facebook suna yiwa mutane Verified din account din su ne, ga iya wa 'yanda s**a cika sharuda ko kuma manyan sanannu a kasa.
A yanzu kuma sun fitar da sabon tsarin da kowa zai iya biyan kudi su mishi Verified, da zaran ka shiga Profile dinka inda ake maida account Professional Mode, a saman wurin za kaga inda aka rubuta Meta Verified kamar yadda zaku gani a hoton da na saka, kana ganin hakan to ka shiga wurin ka biya su bai wuce 4k ba.
Kana biya cikin kwanaki kadan zasu maka Verified, idan ka kasa biya ka tuntubi wa 'yanda suke harkar Crypto su koya maka yadda zaka biya. Idan kuma kaga basu rubuta maka hakan ba, to a yanzu baka cikin list, wata kila nan gaba kadan su bude maka.
Amma tsarin Verified na Page yana da matukar wahala, har yanzu basu fara bada damar mutum ya biya domin su mishi ba, da zaran sun bada damar nima zan biya domin su mini Verified din shafina, ko a yanzu haka na tura musu Request na suyi mini Verified din, wata kila suyi idan sunyi niya.
✍️ Comr Abba Sani Pantami