MI AKE CIKI

MI AKE CIKI Gidan Jarida

Inna lillahi wa Inna Ilaihirraji'unAllah Ya yiwa Mai Martaba Sarkin Sudan na Kontagora Alh Sa'idu Na Maska rasuwa.Allah ...
09/09/2021

Inna lillahi wa Inna Ilaihirraji'un

Allah Ya yiwa Mai Martaba Sarkin Sudan na Kontagora Alh Sa'idu Na Maska rasuwa.

Allah Ya jikansa da gafara.

 Hukumar Kulada Harkokin Sadarwa ta ƙasa (NCC) ta rufe Dukkanin Layukan waya daga Jahar Zamfara na tsawon sati biyu 2 Sa...
04/09/2021



Hukumar Kulada Harkokin Sadarwa ta ƙasa (NCC) ta rufe Dukkanin Layukan waya daga Jahar Zamfara na tsawon sati biyu 2 Saboda matsalar tsaro dake addabar Jahar.

01/09/2021

Yan sanda a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya sun k**a wasu ɗalibai shida kan zargin kutsa kai gidan wani mutum da yi masa askin dole.

Kakakin ƴan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin Dutse.

Ɗan sanda ya shaida cewa an k**a ɗaliban da ake zargi a ranar 27 ga watan Agusta, bayan Ibrahim Sambo, mazaunin unguwar Yalwawa a Dutse ya shigar da kara.

Mutumim ya ce sai da ya yi zazabin kwana biyu bayan faruwar al'amarin.

ASP Lawan ya ce yanzu haka suna rike da ɗaliban da shekarunsu ke tsakanin 18 zuwa 19.

Wadanda ake zargi sun amsa laifinsu, don haka a cewar kakakin za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.

Daga BBC HAUSA

  Daga Jahar KatsinaGwamnan jihar Katsina Right Hon. Aminu Bello Masari ya ayyana dokoki 11 da zasu inganta tsaro a jiha...
31/08/2021

Daga Jahar Katsina

Gwamnan jihar Katsina Right Hon. Aminu Bello Masari ya ayyana dokoki 11 da zasu inganta tsaro a jihar daga ranar 31 ga watan Agusta 2021 har sai yanda hali ya yi .

Dokokin sun haɗa da

1- Ruhe hanyar Jibiya zuwa Gurbin-Ɓore har sai yanda hali ya yi .

2 - Ruhe hanyar Kankara zuwa Sheme ga daukacin motocln haya na gwamnati da na 'yan kasuwa, inda aka basu umurni su bi hayar Funta har sai yanda hali ya yi .

3- Dukan manyan motoci da ke daukar itace a faɗin jihar an dakatar da su har sai an samu cikakken tsaro .

4- An dakatar da siye da siyar da Dabbobi a kananan hukumomin Jibiya, Batsar, Safana, ƊanMusa, Malumfashi, Kankara, Charanchi, Mai-Adua, Kafur, Faskari, Sabuwa, Baure Dutsimma da Kaita .

5- An dakatar da safarar Dabbobi daga daukacin jihar zuwa wasu jihohi .

6- An dakatar da daukar mutum fiye da 2 saman Babur a daukacin jihar

7- An hana siyar da kayan gyaran mashin a kasuwar Charanchi

8- An dakatar da zirga zirgar mashin mai kafa uku da Baburan haya daga karhe Goma na Dare zuwa karhe Shida na Safe a babban birnin jiha, sannan daga karfe Shida na Yamma zuwa Shida na safe a daukacin kananan hukumomin jihar

9- An dakatar da siyar da manfetir a jarkoki daukacin jihar

10- Gidajen manfetir biyu kachal a keɓe da zasu siyar da manfetir sama naira Dubu biyar a kananan hukumomin Jibiya, Batsar, Safana, ƊanMusa, Malumfashi, Kankara, Faskari, Mai-Adua, Kafur, Ɗandume, Sabuwa, Baure, Dutsimma, Kaita, Musawa, Matazu, da Kurfi

11- An yarda ma'aikatan Lahiya, Jami'an tsaro, 'Yan Jarida su yi umfani da ababen hawa mashin mai kafa uku da Babur da gwamnati ta hana a daukacin jihar akowane lokaci

26/08/2021

Domin Alfahari Da Harshen HAUSA, Kawo Mana Karin Magana Guda Ukku Daka Sani?

Kamar Haka
👇👇👇👇
1, Da Sannu Dan Waken Kasa Zai Samu Yaji.

2, Kowa Ya Debo Da Zafi Bakinsa.

3, Abin Da Kamar Wuya Suruka Ta Cinye Surukinta Ranar Aure.

Muna Sauraron Ku.......

Daga Kungiyar "Arewa Media Writers"

Daga

 Yau Assabar an baiwa Mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar Girma, Gwamna Umar Abdullahi Ganduje shin...
21/08/2021



Yau Assabar an baiwa Mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar Girma, Gwamna Umar Abdullahi Ganduje shine ya bada sandar a garin na Bichi.

Photo: BBC Hausa

 Rikici ya barke tsakanin yan ta'addan daji masu satar Mutane a Kaduna inda aka ruwaito sun kashe junansu har lahira.
21/08/2021



Rikici ya barke tsakanin yan ta'addan daji masu satar Mutane a Kaduna inda aka ruwaito sun kashe junansu har lahira.

Al'ummar Jihar Sokoto Suna Fama Da Hare-haren 'Yan Ta'ada, Da Cutar Amai Da Gudawa ..Kungiyar "Arewa Media Writers" tana...
20/08/2021

Al'ummar Jihar Sokoto Suna Fama Da Hare-haren 'Yan Ta'ada, Da Cutar Amai Da Gudawa
..Kungiyar "Arewa Media Writers" tana kira ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar da sauran masu ruwa da tsaki na Jihar dasu gaggauta kai musu dauki.

Daga Kungiyar "Arewa Media Writers"

Kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwan zamani "Arewa Media Writers" karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa Comr Abba Sani Pantami, da shugaban Kungiyar reshen Jihar Sokoto Bashar Mustapha Bashar, tana kira ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Sokoto da masu ruwa da tsaki na jihar Sokoto da ta gaggauta daukar mataki akan irin kisan gilla da ake yiwa al'ummar yankin jihar Sokoto ta gabas musamman kananan hukumomin Goranyo, Sabon Birni, Rabah, Isa, da Wurno don.

Haka zalika wadannan kananan hukumomin suna cikin fargaba da tashin hankali saboda rashin Ingantaccen tsaro hadi da Annobar Amai da Gudawa.

Kimanin kauyuka 30 ne wadanda s**a kaura daga garuruwan su saboda Karancin tsaro a yankunan, haka zalika kusan kullum sai anyi kisa a yankunan, ko a sace musu dabbobi da abincinsu, ko kuma a yiwa matansu da 'ya'yan su fyade.

A cikin wannan makon saida 'yan ta'adda s**a aikawa hakimin garin Makuwana sakon cewa, su gaggauta haɗa musu kudi kimanin naira miliyan daya 1,000,000,00 ko su kori kowa daga garin.

Cikin jimami da fargaba Al'ummar garin s**a hada kuɗaɗen s**a aika musu domin samun zaman lafiya a yankunansu, zuwa yanzu babu wani kauye guda daya daga karamar hukumar sabon birni da ba'a kashe mutane ba tare da kwashe dukiyoyin suba.

Da wannanne muke kira ga gwamnatin Tarayya dama ta jihar sokoto da su gaggauta daukar mataki akan kisan gillar da ake yiwa al'ummar yankin Sokoto ta gabas domin samar da zaman lafiya a Jihar dama yankin Arewa gaba daya.

Ƙungiyar "Arewa Media Writer's" tana yiwa kowa fatan Alkhairi, tare da neman Addu'o'inku akan muhimman ayyukan da tasa gaba.

Rubutawa✍🏻✍🏻✍🏻
Bashar Muhammad Gobir,
Chairman "Arewa Media Writers" Sabon Birni LGA Sokoto State Chapter.

 An daura auren Yusuf Buhari da yar Sarkin Bichi Zahra
20/08/2021



An daura auren Yusuf Buhari da yar Sarkin Bichi Zahra

Auren Ƙasaita  Komai ya kank**a Auren yar Sarkin Bichi da ɗan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Garin Bichi yau Jumu'a
20/08/2021

Auren Ƙasaita

Komai ya kank**a Auren yar Sarkin Bichi da ɗan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Garin Bichi yau Jumu'a

19/08/2021



Wani mutum Yayi barazanar tayar da bomb aginin majalisar Amurka

Ƴan sandan Amurka na gudanar da bincike kan "barazanar harin bam" a kusa da ginin Majalisa a birnin Washington DC.

Ƴan sandan ginin Capitol a Amurka sun ce suna tattaunawa da direban motar da ake zargi na ɗauke da abin fashewar kusa da ɗakin karatu na majalisar da ke gefen t**i daga ginin Capitol da Kotun Ƙoli.

Ba a san manufar direban ba, kuma yana yaɗawa kai-tsaye a cikin motar, k**ar yadda s**a bayyana.

An kwashe ma’aikata da dama da ke aiki kusa da wurin.

Majalisa na gudanar da hutu, amma akwai ma’aikata da ke yin aiki a ginin.

Mutumin ya ajiye motar ne gefen hanya kuma ya shaida wa wani jami’in da ya tunkare shi cewa yana ɗauke da bom, tare da riƙe wata na’ura mai k**a da ta tayar da bom ɗin, k**ar yadda babban jami’in ƴan sandan ginin Capitol Chief J Thomas Manger ya shaida wa manema Labarai

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MI AKE CIKI posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share