03/11/2025
KIM IVERSEN YAR JARIDA A AMURKA TACE...
Shugabannin Amurka suna shirin kaiwa Nigeria yaki ne ba wai saboda ikirarin da suke akan Kiristoci ba, sam sam ba shine dalili ba, kyakkyawar alakar dake faruwa tsakanin Nigeria da Kasar China musamman a bangaren BELT AND ROAD INITIATIVE shine dalili...
Kim tace. ..
Daga farkon shekarar 2025 zuwa yanzu an sanya hannu a yarjejeniyoyin gine gine wadanda darajarsu ta haura dala biliyan 21 wanda hakan ya sa Nigeria zata kasance kasa mafi girma da zata amfana da shirin Belt and Road Initiative a shekarar 2026 zuwa 2030 a Africa..
Sannan Amurka tana da masaniya akan wasu yarjejeniyoyin da aka sanyawa hannu tsakanin China da Nigeria wacce China zata fara ayyukan inganta abubuwan more rayuwa a Nigeria tare da samar da hanyoyin jiragen kasa tsakanin jihohin Nigeria hakan bai yiwa Amurka dadi ba domin tasirin da take dashi zai cigaba da zaizayewa ne a Africa idan ta bari China ta samar da abubuwan more rayuwa a Nigeria..
Akwai wasu sanya hannun da akayi a bangaren Makamashi da Masana’antu tsakanin Nigeria da China wanda shima baiyiwa Amurka dadi ba inji yar jarida Kim Iversen...
Kim Iversen ta karasa da cewa haifar da rudani tare da yaki a Nigeria shine kawai mafita ga Amurka a wannan lokacin don haka ne ta fakaice da maganar Kiristoci take son cimma burinta na lalata shirin Belt And Road Initiative ...
Zamu saka jawabin Kim Iversen cikin harshen Turanci a shafin Biyora Online TV