Mujallar Tunbin GIWA.

Mujallar Tunbin GIWA. SHIRI NA MUSAMMAN DOMIN FADAKAR DA AL'UMMA AKAN TARIHI, RAHOTANNI DAMA TALLACE TALLACE.

13/09/2021
13/09/2021

Wannan shafin zai ke kawo muku bayanai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

13/09/2021

An gano jaririn da aka sace kwana daya da haihuwarsa a Kano.

13/09/2021

Daga fara wasa a United har Ronaldo ya shiga jerin wadanda s**a fi cin kwallaye a Premier League a kakar bana.

13/09/2021

KARE KAI: Shehin Malami a Sokoto Ya Nemi Gwamnati Ta Bashi Bindiga Domin Shiga Daji Don Fatattakar Yan Ta'adda, Ya Kuma Soki Dokokin da Aka Sanya a Sokoto.

Fitaccen malamin addinin musulunci na jihar Sakkwato dake arewacin Najeriya Sheikh Bello Yabo ya bukaci gwamnati ta mallaka masa bindiga tareda hada shi da jami'an tsaro domin ya fatattaki yan ta'adda a dazuka.

A cikin wani dogon bayani na babban malamin wanda ya gudanar a Mumbarin wa'azin sa ya ce, ya damu kan halin matsalar rashin tsaro a jihar da kasar Najeriya.

Sheikh Bello Yabo ya soki gwamnatin jihar Sakkwato kan matakin sanyan dokar hana shiga da fice da itatuwa a cikin mota da kuma haramta cin kasuwannin mako-mako domin dakilar da harkar ta'addanci a jihar.

Babban malamin ya ce, sanya dokar hana shigowa da itatuwa zai jefa al'umma cikin wani hali na kumci. Ya ce sam matakin bai yiba komai bai nuna alamun shawon kan matsalar tsaron.

"Tun harkan nan ta bace, tun da sojoji da jami'an tsaro sun yi kadan mu gamu bamu aikin komai a dauke mu abamu bindiga domin tinkarar yan ta'adda"

"Ire-ire na masu son shiga daji don ceto kasar nan su na da yawa sosai to a bamu dama mana, Amma bai yuwuwa wasu yan tsirarrun mutane sun yi kanfin cikin daji sun gagari gwamnatin Najeriya"~Inji Bello Yabo

Sheikh Bello Yabo ya ce, abin kumya yayi yawa a idon shuwagabannin Najeriya na kin kawo karshen yan ta'adda.

Babban malamin yace, sanya dokar hana shigowa da itatuwan abunci da haramta cin kasuwanni zai janyo matsatsi ga al'umman jihar musamman talakkawa. Ya ce zai dauki iyalansa duka ya kaiwa gwamnan Sakkwato su domin ya ciyar dasu.

13/09/2021

Yan bindiga sun b***e gidan yari sun saki fursunoni 200 a jihar Kogi.

'Yan bindiga a jihar Kogi da ke Najeriya sun ce fursunoni dari biyu da arba'in sun tsere bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari wani gidan yari da ke karamar hukumar Kabba/Bunu da yammacin ranar Lahadi.

Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ta ce maharan da dauke da muggan makamai.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba na cewa an kashe jami'an tsaro biyu.

Rahoto: Comrade Musa Garba Augie.

06/09/2021
31/08/2021

Amarachi Okeh Rivers, the Federal Capital Territory, and 12 other states reported 460 new cases of COVID-19 on Monday, according to figures released on Tuesday by the Nigeria Centre for Disease Control. The health agency also reported one COVID-19 related death. The NCDC disclosed this on its offici...

31/08/2021

Tension has gripped residents of Sapele, Sapele Local Government Area of Delta State as Hausa traders and Fulani herders in the area on Monday engaged in a bloody clash

31/08/2021
31/08/2021

Taliban spokesman says Afghanistan has ‘gained complete independence’ as fighters enter hangars occupied by US forces hours earlier

Address

No 45c Guiwa Low-cost Area Sokoto
Sokoto

Telephone

+2348135441114

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mujallar Tunbin GIWA. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Mujallar Tunbin GIWA.:

Share