
24/06/2025
Bazamu saki jika da wadanda tun zuwan Musulunci suke karya Alkawari ba.
_Faruk Sidi Attahiru
A tarihin Musulunci, Manzon Allah (s.a.w.w) ya yi sulhu da wasu ƙabilun Yahudawa a Madina da kewaye, Amma da yawa daga cikinsu sun warware alkawari ko yin cin amana.
Bari mu dauki Darasi daga yin sulhu da jerin wasu daga cikin manyan ƙabilun Yahudawan da hakan ya faru da su:
1. Banu Qaynuqa‘a
Sulhu Bayan hijira zuwa Madina, Manzon Allah (s.a.w.w) ya amince da zaman lafiya da su a cikin Sahifatu Madina
Sun warware Sulhu Bayan da s**a keta doka da tozarta wata Musulma a kasuwa, Manzon Allah ya kai musu hari, aka ci su da yaki, aka kore su daga Madina.
Acikin Suratul Hashr, Aya ta 2, Allan ta'ala yana cewa:
"هُوَ الَّذِي أَخْرَجَ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ مِن دِيَارِهِمْ لِأَوَّلِ الْحَشْرِ ۚ مَا ظَنَنتُمْ أَن يَخْرُجُوا وَظَنُّوا أَنَّهُم مَّانِعَتُهُمْ حُصُونُهُم مِّنَ اللَّهِ فَأَتَاهُمُ اللَّهُ مِنْ حَيْثُ لَمْ يَحْتَسِبُوا وَقَذَفَ فِي قُلُوبِهِمُ الرُّعْبَ يُخْرِبُونَ بُيُوتَهُم بِأَيْدِيهِمْ وَأَيْدِي الْمُؤْمِنِينَ فَاعْتَبِرُوا يَا أُولِي الْأَبْصَارِ"
Ma'ana: Shi ne (Allah) wanda ya fitar da waɗanda s**a kafurta daga Ahlul Kitab daga gidajensu a farkon korarsu. Ba ku yi tsammanin za su fita ba, su kuma sun yi zaton katangunsu za su hana su (azabar) Allah. Amma Allah ya zo musu daga inda ba su zata ba, kuma Ya jefa tsoro a zukatansu. S**a rusa gidajensu da hannayensu da kuma hannun muminai. To ku dauki darasi, ya ku masu basira.
2. Banu Nadir
Anyi sulhu da yarjejeniya tsakaninsu da Musulmi don zaman lafiya.
Daga baya s**a warware sulhu sunyi yunƙurin kashe Manzon Allah (s.a.w.w), sai aka kewaye su, s**a mika wuya, aka kore su daga Madina zuwa Khaybar.
A cikin Suratul Anfal, aya ta 56 Allah ta'ala yana cewa:
"الَّذِينَ عَاهَدتَّ مِنْهُمْ ثُمَّ يَنقُضُونَ عَهْدَهُمْ فِي كُلِّ مَرَّةٍ وَهُمْ لَا يَتَّقُونَ"
Ma'ana: "waɗanda ka yi yarjejeniya da su, sai su keta yarjejeniyar a kowane lokaci, kuma ba su jin tsoron Allah"
3. Banu Qurayza
Suma anyi sulhu dasu kuma sun kasance cikin yarjejeniyar sahifatu Madina.
Still suma s**a warware Sulhu, A lokacin yaƙin Khandaq, sun ci amanar Musulmi ta hanyar haɗin guiwa da maƙiya (Quraysh da Ahzab). Bayan nasarar Musulmi, aka kewaye su, aka yanke musu hukunci bisa dokarsu.
A suratul Ma'ida, aya ta 13, Allah madaukakin sarki yana cewa:
"فَبِمَا نَقْضِهِم مِّيثَاقَهُمْ لَعَنَّاهُمْ وَجَعَلْنَا قُلُوبَهُمْ قَاسِيَةً ۖ يُحَرِّفُونَ الْكَلِمَ عَن مَّوَاضِعِهِ وَنَسُوا حَظًّا مِّمَّا ذُكِّرُوا بِهِ ۚ وَلَا تَزَالُ تَطَّلِعُ عَلَىٰ خَائِنَةٍ مِّنْهُمْ إِلَّا قَلِيلًا مِّنْهُمْ ۖ فَاعْفُ عَنْهُمْ وَاصْفَحْ ۚ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ"
Ma'ana: "saboda sun karya alkawarinsu, Mun la’ane su, Mun kuma sanya zukatansu masu tauri. Suna karkatar da kalmomi daga inda aka ajiye su, kuma sun manta da wani ɓangare na abin da aka tunatar da su. Kuma za ka ci gaba da samun cin amana daga cikinsu, sai kaɗan daga cikinsu. To ka gafarta musu, ka yi afuwa. Lallai Allah yana son masu kyautatawa.
Ayoyin nan suna nuni da irin waɗanda Manzon Allah (S) ya yi sulhu da su, amma a kai a kai suke karya yarjejeniyar, su taimaki maƙiyan Musulmai, su shiga yaƙi a bayyane ko a ɓoye.
A cikin tafsirin Al-Meezan na Allama Tabataba’i ya bayyana cewa: wannan irin rashin gaskiya da karya alkawari yana daga siffofin ɗabi’ar Yahudawa a tarihi, kuma wannan aya tana umarni ga Musulmi su kasance masu wayo wajen ma'amala da irin waɗannan mutane, su rika kula da amintaka da tsaro.
DARASI: Kada Musulmi ya yarda da wanda ya saba karya yarjejeniya, musamman idan addini da rayuwar al’umma na cikin haɗari. Tun kafa haramtacciyar Isra'ila ba'a taba yarjejeniya da ita ko sulhu batareda ta karyashi ba.
Allah yasa mu hankalta yakuma cigaba da bama Jamhuriyyar Musulunci ta Iran kariya yakuma shiga Al'amarinta tareda dubun kariya ga Jagoranta Sayyid Ali Khamena'i (H).