Pharm Muhammad Imam

Pharm Muhammad Imam I'm Muhammad muhuyiddin nasir sabon birni local government, sokoto state, Nigeria.

18/04/2024
πŸ’―πŸ’―πŸ’―At school 🀲🀲🀲
22/02/2024

πŸ’―πŸ’―πŸ’―At school 🀲🀲🀲

Wallahi mukikayi hassada da ciutarwa!Aduk lokacinda kayi kokarin ciutamasa sai Allah yadaukakashi da wannan ciutarwa,Adu...
09/01/2024

Wallahi mukikayi hassada da ciutarwa!
Aduk lokacinda kayi kokarin ciutamasa sai Allah yadaukakashi da wannan ciutarwa,Aduk lokacinda kayi kokarin sannesa sai Allah yadaukakashi.
ALLAH YAKAREMU DAGA HASSADA!

Kada kazama mai nuna damuwarka akowane lokaci kawai k**aida al'amarinka zuwa ga mahaliccin ka
26/11/2023

Kada kazama mai nuna damuwarka akowane lokaci kawai k**aida al'amarinka zuwa ga mahaliccin ka

Kayi abunda kasan cewa zai anfaneka koda nan gabane SannanKabar abunda kasan bazai anfanekaba koda nan gabane!
17/10/2023

Kayi abunda kasan cewa zai anfaneka koda nan gabane
Sannan
Kabar abunda kasan bazai anfanekaba koda nan gabane!

04/10/2023

Kai Ζ΄an Ι—ariqa!!
Indai ku masu gaskiyane akan sonda kukeyiwa Annabi to duk abunda zaku fada lalle yakasance Annabine yafada ko ayan alqur'ani ne da fassara mai kyau!

26/09/2023

Follow our channel on WhatsApp

πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

25/09/2023

SAI DA NA ZUBAR DA HAWAYE DA NA KARANTA LABARIN NAN πŸ˜₯

~ Muna zaune muna tattaunawa da safe k**ar karfe 9 na safiyar ranar Laraba 20 ga watan September 2023 da kanwar Mahaifina, muna magana har dai hirar ta kaimu ga zancen wani mutum Bawan Allah, sai take sanar dani cewa an zalunce shi, an cutar dashi, an 'daure shi a Gidan Yari na tsawon shekaru 4 zai shiga shekara ta biyar a yanzu haka.

~ Nan da nan na tashi naje Gidan Yarin, na nemi izini ina son ganin sa, aka yi mun duk binciken da za'a yi, na cike duk wata ka'idar ganin mutum a Gidan Yarin, na shiga na ganshi, yana fitowa sai na ganshi da Haiba, Kamala, da Cikar fuska, yana sanye da Gilashi a Idon sa, Saurayi cikakke abun burgewa.

Sai na tattauna dashi, tattaunawar gata k**ar haka:

Nace 'dan uwa ya kake, yace lafiya lau Malam, Alhamdulillah, nace muna zaune da Hajiya (.....) muna tattaunawa sai muka biyo kan labarin ka, sai take ban labarin ka, wallahi ban san ka ba, ban san labarin ka ba sai yau (Laraba 20 September 2023).

~ Yace Allah Sarki, sannu da zuwa, nace yauwa. Nace 'dan uwa shekarun ka nawa? sai ya fada mun sai naga ai kusan shekaruna da nasa 'daya ne. Nace shekarun ka nawa a Gidan Yarin nan, yace hudu tun 2019.

Nace me ya faru har kazo nan? yace sharri aka yi mun, wata mata ce tayi mun sharri, cewa wai na nemi nayi lalata da ita, alhali karya ne. Mijin ta babban mutum ne yana Kudi, sai kawai aka k**a ni aka daure ni, ina zaune a nan shekaru hudu. Nace a lokacin da aka k**a ka kana karatu ne? Yace eh ina karanta Law har na kai 400 level a University.

~ Nace a ina ka hadu da matar har tayi maka wannan Qazafi? yace ina koyar da 'ya'yan su Al-Qur'ani da Hadisai ne a gidan su ana biya na duk wata, sai tayi mun wannan Qazafi.

Nace anyi bincike akai, yace Eh anyi, an tabbatar bani da laifi, anje gaban hukuma, anje Kotu, shine s**a ce a daure ni, ni kuma na karbi Qaddarar. Daga baya tazo tace wa Mijin ta wallahi wallahi karya tayi, sharri tayi mun, ta kira Mama na a waya tace kiyi hakuri sharri nayi wa 'danki.

~ Nace yaushe tayi haka? yace bayan shekara daya da shigowa ta Gidan Yari, yanzu shekaru uku da gano gaskiyar Amma ana rike da Kai? yace Eh.

Jama'a babban abinda zai baku mamaki sune wasu abubuwa guda 6 dana Ciro su daga tattaunawar mu:

1. Na farko Mahaddacin Al-Qur'ani ne.

2. Na biyu, wannan Sallar Layyar data wuce Mahaifiyar sa tayi masa dinkin sallah kala Goma zata kawo masa Gidan Yarin sai Mota ta buge Mahaifiyar sa, nan take ta rasu.

3. Matar da tayi masa sharrin Zina yanzu haka ta makance bata gani da Idon ta.

4. Mijin ta yayi Hatsari, an yanke masa 'kafa yanzu haka.

5. Matar da tayi masa sharrin tana da 'Ya'ya uku, sunyi tafiya (su Yaran) s**a yi hatsari a Mota, wata Trailer ta markade su gaba daya s**a mutu, su Yaran.
Bala'i da fitin-tinu kullum Hawa kan matar suke yi, tana kasuwanci yanzu kasuwar ta rushe bata da komai.
(matar tayi ta aikewa da sako cewa don girman Allah ya daina yi musu addu'a haka, sun ga bala'i iri iri a shekaru hudun nan, yayi hakuri ya yafe mata).

6. Yace mun, saboda an tabbatar baya da laifi har an bashi dama yayi Degree daga Gidan Yarin, ya kammala yanzu haka yana masters dinsa. Yana business dama, ya samu wasu matasa masu gaskiya da Amana sun rike masa Kasuwancin sa da gaskiya.

Nace me yasa matar ba zata zo ta saka hannu ta tabbatar sharri tayi maka ba, yace suna tsoro ne, bayan sun wahalar dani yanzu idan s**a dawo s**a ce karya s**a yi ita matar za'a k**a a daure. Kuma matar babban mutum ne, Asirin su zai tonu, zasu ji kunya.

~ Yace abinda aka yi guda 'daya ne, shine an rubuta sunana daga cikin wadanda Gwamna zai yafe musu, irin Afuwan nan da Gwamnati take yiwa 'yan Gidan Yari duk shekara, toh an Saka sunana, muna zaton a cikin watan October mai zuwa 2023 din Nan za'a fitar dani.

~ Nace me kake so yanzu nayi maka na taimako?
Yace Ina so ka taya ni addu'a. Nace bayan wannan fa? Nima field dinka na karanta Law nayi, yace ma sha Allah, yanzu mun tsallake wajen da ake bukatan Lauyoyi, Gwamnati ne kawai muke jira ta yafe mana.

~ Wani abun mamaki kumaπŸ‘‡

~ Nace masa an bani Lambar wayar budurwar ka tun kafin nazo nan, nayi waya da ita, itace ma tayi ta taimaka mun har na shigo nan, yace Allah Sarki. Yarinya ce karama, ta tsaya sai shi din, tayi hakuri tsawon shekarun nan, iyayen ta sun karfafe ta akan sa, cewa tayi hakuri, tace babu komai, idan ya fito za suyi aure.
~ Yace yanzu kaga a gidan Yarin nan na Haddatar da mutane da yawa Al-Qur'ani, da yawa sun san Musulunci sun shiryu. Yacmun yana Azumin Litinin da Al-Hamis duk Sati, kuma yana tsayuwan dare, yace babu wata mummunar addu'a da yake yi ma wancan matar, jarabawar Allah ne kawai yake hawa kanta.

Yace Barrister menene sunan ka, ina so mu saba...

```KISSA MAI CIKE DA ABUBUWA!!! A zamanin khalifa Umar dan Khattaab, wasu mutane uku s**a zo masa suna rike da wani saur...
23/09/2023

```KISSA MAI CIKE DA ABUBUWA!!!

A zamanin khalifa Umar dan Khattaab, wasu mutane uku s**a zo masa suna rike da wani saurayi s**a ce:
Ya Amiral muminina! Wannan mutum ya kashe mana mahaifinmu.

Umar: kai donme ka kashe musu uba?

Saurayi: Ni makiyayi ne, rakumata ce ta ci itaciyar gonar mahaifinsu, sai mahaifinsu ya bugi rakumin da dutsi, rakuma ta mutu, ni kuma na dauki dutsin na buge shi
ya mutu.

Umar: saboda haka zan tsaida haddi akanka.

Saurayi: ka saurara mini kwana uku, mahaifina ya mutu ya barni da kanwata da
kuma dukiya, idan ka kasheni dukiyar da yar uwata zasu tozarta.

Umar: wa zai lamunceka?

Saurayi ya duba cikin mutane sai ya nuna Sahabi "Abu Dhar".

Umar: ka lamunce masa Ya Aba Dharr?

Abu Dharri: na'am

Umar: ba ka san mutum ba ka lamunce, to idan ya gudu haddi zai koma kanka.

Abu Dharr: na yarda.

Saurayi ya tafi, aka kwana biyu, an shiga na so uku, saurayi bai zo ba,

Hankalin kowa ya tashi akan Abu Dharri kar haddi ya koma kansa.

Kafin sallar magariba sai ga saurayi ya zo a gajiye, ya tsaya a gaban khalifa Umar.

Saurayi: na mika dukiyar ga kawuna yanzu ina hanunka, ka tsaida haddi
akaina.

Cikin mamaki Umar ya ce: me ya dawo da kai bayan ka sami dama da za ka
iya gudu abinka?

Saurayi: na ji tsoro, Kar a ce cika alkawari ya Kare
cikin mutane.

Umar ya juya ga Abu Dharr: me ya sa ka lamunce
masa?

Abu Dharr: na ji tsoro, kar a ce alheri ya Kare cikin
mutane.

Wannan jawabi ya yi tasiri ga masu Neman jinin ubansu, s**a ce sun yafewa
saurayi.

Umar: don me?

S**a ce: muna tsoro, kar a ce afuwa ta Kare a cikin mutane.

Ni ma na isar maka da wannan labari ne don ina tsoron kar a ce kira/tunatarwa zuwaga aikata alkhairi (wato da'awa) ya Kare cikin mutane. Don Allah kai ma ka tura kar ace yada alheri ya qare cikin mutane. ```

Address

Sabon Birni Local Government
Sokoto
1357

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Pharm Muhammad Imam posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Pharm Muhammad Imam:

Share