11/15/2025
Idan kana son ka fara samun kuɗi daga Facebook, ka kula da waɗannan abubuwa:
1. Ka daina satar bidiyo ko hoton wani – Facebook baya amincewa da duplicated content. Yi naka abu daga tushe.
2. Ka dinga saka bidiyo masu tsawo (3 min+)
3. Ka zaɓi niche guda daya (kamar cooking, comedy, knowledge, motivational e.t.c) ka tsaya a kai.
4. Ka kasance da posting consistency – a kalla 3–5 posts a mako.
5. Ka gina audience na gaskiya – kar ka dogara da fake followers ko buying likes ko follow for follow
6. Ka guji kalaman cin zarafi, siyasa mai zafi, da tashin hankali – suna iya hana monetisation.
8. Ka bi Community Standards da Partner Monetisation Policy sosai.
9. Ka koyi basic editing domin ka rika yin bidiyo masu kyau suna jan hankali.
10. Ka yi haƙuri – monetisation ba sa zuwa nan take.