
19/07/2025
A wani mataki na bunkasa shirye-shiryen abinci mai gina jiki, Hukumar Kula da Lafiya matakin farko ta Jihar Sakkwato ta hanyar Sashen kula da abinci mai Gina Jiki tare da hadin gwiwar ofishin asusun yara na majalisar dunkin duniya na Sokoto, sun gudanar da taron kwana biyu na tantance daidaitattun hanyoyin sauya dabi’u wanda akayi a Jihar Kebbi.
Taron ya mayar da hankali ne wajen duba da daidaita takardun da s**a shafi abinci mai gina jiki, domin kara inganci da tasirin shirye-shiryen gina jiki a fadin Jihar Sakkwato.
A yayin bude taron, Kwamishinan Lafiya na Jihar Sakkwato, Dr. Faruk Umar Wurno, wanda babban Sakatare na Ma’aikatar Lafiya, Ibrahim Haliru Dingyadi, ya wakilta, ya bayyana muhimmancin tabbatar da daidaito da inganci a dukkan ababen gina jiki.
Yace Daidaita kayan aiki na tabbatar da cewa Jihar Sakkwato ta zama abin koyi a fannin shirye-shiryen abinci mai gina jiki.
A nasa jawabin Daraktan Lafiyar Al’umma, Dr. Tukur Garba Magaji, ya jaddada muhimmancin wannan taro wajen kara fadada isar da ayyuka zuwa al’ummomi, musamman masu karancin samun kulawa.
Daraktan yace Taron nan yana taimakawa wajen inganta isar da shirye-shirye ga wadanda ke bukatar hakan da gaske, musamman a kauyuka da ke da karancin kula.
Acewar wata sanarwa daga Ibrahim Iya, jami’in yada labarai na ma’aikatar lafiya ta bayyana cewa taron ya hada manyan masu ruwa da tsaki domin daidaita dabaru da kuma daidaita shirin jihar sokoto da ka’idojin duniya.
Shima Ibrahim Haruna, wanda ya wakilci Shugaban ofishin UNICEF Mista Michael Juma, ya tabbatar da ci gaba da goyon bayan UNICEF ga kokarin Jihar Sakkwato a fannin gina jiki.
Ayo Bami na kungiyarsu Nutrition International ya bayyana sakon fatan alheri a madadin abokan hadin gwiwa, inda ya yabawa hadin gwiwar da ke tsakanin gwamnatin jihar Sokoto da UNICEF, yana mai bukatar a ci gaba da zuba jari a bangaren lafiyar yara.